Abin da ya sa muka rinƙa ciyo bashi a shekaru takwas na mulkin Buhari – Minista

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari mai barin gado ta kare matakin da ta ɗauka na ciwo basussuka masu ɗimbin yawa a ciki da wajen ƙasar a shekaru takwas da ta shafe ta na mulki.


Basussukan da ƙasar ta ciyo ya sa wasu ‘yan Nijeriya da masana tattalin arziki sun nuna damuwa a kan matsalolin da ƙasar za ta iya fuskanta sakamakon yawan basussukan.

Sai dai Ministar Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki ta Ƙasa ta Nijeriya, Zainab Shamsuna Ahmed ta shaida wa BBC cewa gwamnati ta karvo bashin ne domin hana ƙasar faɗawa cikin mawuyacin hali a lokacin da ƙasar ta samu koma bayan tattalin arziki a shekarun 2016 da 2020.

“Mun samu durƙushewar tattalin arzikin ƙasa sau biyu, a 2016 da 2020 lokacin annobar Korona, mun yi iya ƙoƙarinmu wajen ganin ƙasar ba ta faɗa cikin mawuyacin hali ba.

“Saboda ƙasa mai girma irin Nijeriya idan aka barta cikin wannan hali, abin zai ɓaci ne, nesa ba kusa ba,” inji ta.

Ministar ta kuma ƙara da cewa a lokacin da suka karɓi ragamar mulki a shekarar 2015 kasafin kuɗin ƙasar ya kai Naira tirili ‘yan 4.5 amma a wannan shekarar kasafin kuɗin ƙasar ya kai Naira triliyan 21.5

A cewarta ba ‘yan gyaran da suka yi wa kasafin kuɗi daga watan Janairu zuwa Disamba sun kuma aiwatar da wasu tsare-tsare domin tabbatar da adalci wajen aiwatar da kasafin kuɗi.

“Mun shigo da hanyar gyara hanyoyin da ke barin ana barvar kuɗin, kuma waɗannan mun yi su ne ta cikin tsarin shari’a da ake kira ‘finance bill’.

“Sun taimaka mana mun samu ƙarin kuɗin shiga wa gwamnatin tarayya, daga tirili ‘yan 3 zuwa tirili ‘yan 10.7 a bara.”

Zainab Shamsuna ta kuma ce gwamnati ta sauya fasalin kuɗin da ke shigowa.

A cewarta da farko kashi 70 cikin 100 na kasafin kuɗin ƙasar ya dogara ne a kan man fetur amma a yanzu kashi 65 cikin 100 na kasafin kuɗin ana samunsa ne daga ɓangaren da ba na man fetur ba.

Ministar ta kuma ce durƙushewar tattalin arzikin da aka samu a lokacin ɓullar annobar Korona ta sa gwamnati sake ciyo bashi.

Sai dai a ƙarƙashin mulkin Shugaba Buhari ne aka samu tashin farashin kayayyaki da faɗuwar darajar Naira da kuma ta ƙarawa ƙasa ɗimbin bashi ko da yake ministar ta kare matakin.

“Ba mu ne kaɗai mu ke da bashi ba, babu ƙasar da ba ta neman bashi, mun kuma sami shugaban ƙasa da yake cewa ku amsa domin a yi man ‘yan ayyuka.’’

Game da tashin farashin kayayaki kuwa ministar ta ce ba Nijeriya kaɗai ba ce matsalar ta shafa.

A cewarta matsalar na da nasaba da yaƙin Ukraine da kuma annobar Korona.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *