Abin da ya sa na keta maƙogoron abokin karatuna, cewar ɗalibin sakandare a Maiduguri

Daga BASHIR ISAH

Rundunar ‘yan sanda a jihar Borno ta cafke wani matashi mai suna Umar Goni ɗan shekara 16, kuma ɗalibi a makarantar ‘Elkanemi College of Islamic Theology Maiduguri’, bisa yunƙurin halaka wani ɗalibi abokin karatunsa mai suna Jubril Mato.

Tun farko, jaridar Neptune Prime ta rawaito labarin yadda Umar Goni ya keta maƙogoron abokin karatunsa Jubril Mato, dan shekara 12, da makami a nan makarantar tasu.

Daga bayanan da ya yi wa ‘yan sanda, Goni ya yi iƙirarin cewa ya aikata wannan ɗanyen aiki ba don komai ba, sai don neman iyayensa su cire shi daga tsarin kwana a makaranta.

A cewarsa ya sha faɗa wa iyayen nasa a kan su cire shi daga tsarin kwana a makaranta amma ba su saurare shi ba, shi ya sa ya aikata abin da ya aikata ɗin don tilasta wa iyayensa cika masa buƙatarsa.

Matashin ya ce ya yi matuƙar nadama da abin da ya aikata wanda haka ya sanya shi roƙon afuwa kan aika-aikar tasa, tare da yin fatan samun lafiya cikin gaggawa ga abokin karatun nasa da ya keta wa maƙoshi.

Jubril Mato

Kawo yanzu dai Gwamnatin Jihar Borno ta ce za ta kafa kwamiti na musamman don gudanar da bincike kan harin da Goni ya kai wa Mato ɗan aji ɗaya (JSS1) wanda dukkansu biyun ɗaliban El-Kanemi College of Islamic Theology ne a Maiduguri.

Sa’ilin da yake tsokaci kan lamarin a Juma’ar da ta gabata, Kwamishinan Ilimi na jihar, Lawan Abba Wakilbe, ya bayyana lamarin a maatsayin abin takaici, tare da cewa Goni na hannun ‘yan sanda ana ci gaba da tsare shi.

Kwamishinan ya ce za su sanar da duniya halin da ake ciki game da batun bayan kwamitin binciken da aka kafa ya kammala aikinsa.