Abin da ya sa Wazirin Katsina, Sani Abubakar Lugga ya ajiye muƙaminsa

Daga WAKILINMU

A ranar Alhamis da ta gabata Wazirin Masarautar Katsina, Alhaji Sani Abubakar Lugga ya ajiye muƙaminsa na Wazirin Katsina.

BBC ta rawaito Sarkin Yaƙin Masarautar Katsina, Alhaji Ibrahim Ifo na cewa Masarutar ce ta fara aike wa wazirin takardar neman bayani kan wasu kalamai da ya yi a birnin Ilori na jihar Kwara.

Wazirin Katsinan ya yi jawabi ne a wajen wani taro kan matsalolin tsaron da jihar Katsina ke fama da su, inda ya ce ikon ƙananan hukumomi bakwai ba su hannun gwamnati, kuma hakimai da shugabanni sun yi ƙaura daga yankunan zuwa cikin birnin Katsina, kuma cewa an rufe makarantu a yankunan.

Sarkin Yaƙin ya ce ko da aka aika wa wazirin saƙon sai ya aiko da takardar ajiye aiki kafin ya bayar da amsa kan bayanin da aka nemi ji daga bakinsa.

Alhaji Ibrahim Ifo ya ce masarautar ta Katsina ta nemi ƙarin bayani daga bakin Alhaji Lugga ne saboda bayanan da ya yi a Ilori sun tayar da hankula a jihar.

“Sannan kuma wasu abubuwan da ya faɗa ba daidai ba ne. A matsayinsa na mai riƙe da babbar sarauta ya kamata duk abin da zai faɗa da ya shafi jama’a ya zama masarauta na da masaniya a kansu. Ba mu tura masa takardar neman bayani da nufin tozarta shi ko cin mutuncinsa ba,” in ji Alhaji Ifo.

Sakataren masarautar ya ƙara da cewa daga baya Alhaji Lugga ya aika da takardar amsa kan bayanin da aka buƙata daga wajensa, inda ya ce ya yi bayanin ne a matsayinsa na Alhaji Lugga ba na Wazirin Katsina ba.

A yanzu haka Alhaji Ifo ya ce masarautar Katsina ta mashi buƙatar yin murabus ɗin wazirin, kuma nan ba da jimawa ba za a naɗa sabon waziri.