“Matsalar aure da na shiga ta sa ni kafa ƙungiyar taimakawa mata”
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Masu hikimar magana na cewa, ciwon ‘ya mace na ’ya mace ne. Kuma abu namu maganin a kwaɓe mu. Wannan duk maganganu ne na azanci da ake jingina su ga mata. Duk kuwa da cewa da ake yi mata ba su cika son junansu ba, ko nuna goyon gaba da tausayawa ‘yan uwansu mata ba. Amma wannan zargin bai cika zama gaskiya ba, domin kuwa ana samun mata da ke nuna tsananin tausayawa da tallafawa ga ‘yan uwan su, sakamakon wata jarabawar rayuwa da suke fuskanta. Hajiya Aishatu Abubakar Abdullahi da aka fi sani da Sayyida Aisha, wata jajirtacciyar mace ce mai kishi, da tausayi, da son taimakawa al’umma, da ke zaune a Filin Sukuwa a cikin garin Jos. Tsayuwar dakar da ta yi wajen aikin tallafawa zawarawa da marayu ne ya sa ta kafa Gidauniyar Al-Hablul Mateen, wacce a dalilin ta mata da matasa da yara marayu masu yawan gaske ne suka amfana, kuma rayuwarsu ta inganta. Wakilin Blueprint Manhaja a Jos, ABBA Abubakar Yakubu, ya zanta da wannan baiwar Allah wacce ta kasance ‘yar kasuwa, mai aikin ba da magani, mai hidima kan harkokin Ɗariƙar Tijjaniyya, kuma marubuciyar littattafan faɗakarwa.
MANHAJA: Ina son ki gabatar mana da kanki.
SAYYIDA AISHA: To, ni dai sunana Aishatu Abubakar Abdullahi wacce aka fi sani da Sayyida Aisha Filin Sukuwa. Ni ce shugabar Gidauniyar Tallafawa Zawarawa, wato matan da suka rasa mazajen su da kuma yara Marayu, ta Al-Hablul Mateen Foundation. Ni uwa ce ina da aure na da yarana shida, huɗu mata biyu maza. Ni ‘yar kasuwa ce, kuma mai ba da taimako ta fuskar magungunan gargajiya. Ni haifaffiyar Jos ce, kuma na taso a Sabon Fegi, Layin Mudi Na Garba.
Yaya batun harkar karatu kuma?
To, Alhamdulillahi. Ni dai ban samu dama na yi wani zurfin karatu ba, na dai tava karatu na Islamiyya. Na yi karatu a makarantar allo, zuwa makarantar dare, da kuma makarantar Islamiyya ta Asabar da Lahadi, a nan Mubarakatul Islam. Na kuma yi karatun Diploma ta NCE a ɓangaren Arabiyya, a makarantar Higher Islam ta Fauƙa duk a nan Jos.
Wacce gwagwarmaya ki ka sha da ta canja miki rayuwa?
To, ita rayuwa dama tana cike da ƙalubale sosai, kuma wannan ne ma ya zaburar da ni don kafa wannan ƙungiya, domin in ga na tallafa wa matan da suke fuskantar ƙalubale irin nawa. Na samu matsalar rayuwa a baya ta dalilin zaman aure, sakamakon bambancin ƙabilar da na fito da wacce mijina ya fito, domin ni bahaushiya ce gaba da baya, shi kuma bayarabe ne. Sai yake ƙoƙarin tafiyar da ni yadda zamantakewar auren Yarabawa ta ke, a dalilin haka muka riƙa fuskantar savani da shi, kafin muka fahimci juna. A baya har ta kai ga mun raba ɗaukar ɗawainiyar karatun yara, da wasu nauye nauyen iyali, duk kuwa da bani da ƙarfin hakan, sai kuma ya tafi ya bar ni da su, komai kuma ya dawo kaina, sai lokacin da ya bushi iska ya zo, tun bayan da ya yi ritaya daga aiki.
Ba ƙaramin faɗi tashi da buga buga na sha ba, har dai yarana suka kai matakin karatu a jami’a. Da taimakon Allah da tallafawar wasu bayin Allah haka na iya biyan kuɗin karatunsu, har suka samu ilimin da wasu yaran masu gata ma, ba su samu ba. Bayan Allah ya nufe ni da samun natsuwa a rayuwa, inda har na gina muhallin kaina. Shi ne ni ma na ga ya kamata ko ɗan yaya ne in riƙa tallafawa wasu da ba su da damar da ni yanzu na samu.
Yaya aka kai ga kafa wannan ƙungiya?
To, a gaskiya tarihin kafuwar wannan ƙungiya ta Hablul Mateen ya na da ɗan tsayi, domin abin ya fara ne a hankali, daga matakin kwamitin Mauludi na gidana, kasancewar ni ‘yar Ɗariƙar Tijjaniyya, ina shirya taron Mauludi a gidan ana zikiri da ƙasidun yabon manzon Allah (SAWA) da girmamawa ga waliyai. To, duk lokaci idan ya zago akwai kwamiti da na shirya wanda ke tattauna yadda taron zai gudana da abubuwan da za a gudanar na hidimar Mauludin. To, a cikin tsare tsaren namu akwai ba da tallafi ga marayu da mabuƙata. Wata rana na yi wani baƙo wanda ba Musulmi ba ne, ana ce masa Pastor Elisha daga ECWA ta Ɓukur, ya zo gidana sai ya ga jama’a an cika ana ta hidima, shi ne ya ke tambayata mene ne mu ke yi haka?
To, da na bashi labarin abin da muke yi sai ya nuna jin daɗi sa da abin, har ma kuma ya bani shawarar in mayar da kwamitin ya zama qungiya mai rijista. Kuma in nemi shawarar manyan unguwa, da jagororin mu na addini, domin su ba ni shawarar da ta dace. Da wannan shawara ta shi ne muka kai ga kafuwar wannan ƙungiya ta Hablul Mateen, kuma har muka kai ga yi mata rijista, da faɗaɗa ayyukan da muke yi na ba da tallafi.
Kawo yanzu mutum nawa ne suka amfana da ayyukan jin ƙai da ku ke yi?
Gaskiya mun yi aikace-aikace da da yawa, na farko dai mun fara ne da ɗaukar nauyin ɗinkin Sallah ga yara maza marayu, saboda su maza ba su da ɗawainiya da yawa kamar mata, duk da ya ke dai akwai tallafin da su ma muke ba su. Amma dai mun fara da maza ne, sannan muka shiga ɗaukar nauyin karatun yara marayu, inda muke neman masu makarantu su ba mu guraben kai marayu da za su bai wa tallafi a makarantunsu, ko kuma zabtare wani abu daga kuɗin makaranta ba da za mu iya cikawa mu bayar don su yi karatu, yanzu haka wasu yaran har sun shiga sakandire. Akwai kuma tsarin tallafin koyar da sana’o’in hannu na mata, don tallafawa rayuwar gwagwaren mata da suka rasa mazajen su na aure.
Muna kuma ba da shawarwari da shiga tsakanin ma’aurata da suka samu saɓani, don gyara yadda auren zai koma daidai a kaucewa mutuwar aure da ƙaruwar zawarawa, da yara ƙanana marasa samun kulawar iyaye, da ke girma su gagari jama’a. A taƙaice ce dai mun tallafawa mata da yara sun fi dubu biyu, daga kafuwar ƙungiyar shekara biyu kenan. Waɗanda suka amfana da ayyukan aungiyarmu, ba a Jos ko Jihar Filato kaɗai suka tsaya ba, har ma da wasu yankuna a jihohin Bauchi da Gombe.
Daga ina ku ke samun kuɗaɗen da ku ke gudanar da ayyukan nan da ku ke yi?
To, gaskiya ni da na fara wannan aikin ni kaɗai nake abu na, ɗan taro da sisin da na haɗa shi ne nake sa wa a yi min ‘yan ɗinkuna mu raba wa marayu. Daga bisani kuma muka haɗu da wasu ‘yan ƙungiya da tun a lokacin suka nuna min sha’awarsu ta shiga cikin wannan aikin ladar, daga ciki akwai, Malam Abubakar Isa Mari, sai wani Malam Muhammad Kabir, wata ‘yar ɗakina Aishatu Salihu, waɗannan su ne muka fara tafiyar da wannan aiki tare da su, kowa yana ba da gudunmawa daga aljihunsa, ana sayen abin da ake buƙata don a bayar ga waɗanda Allah ya shirya za su amfana.
To, sai kuma sauran mutanen gari ɗaiɗaikun, Musulmi da waɗanda ba Musulmi ba. Musamman wani uban ɗakina, wanda shi ma Kirista ne da ke Cocin fadar gwamnatin Jihar Filato, Rabaran Hussaini Gotom, akwai Pastor Benji wanda shi ma Kirista ne, da akwai Barista Muhammad Abdulrahman na Babbar Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Jos, sai kuma uwa uba Marafan Gombe Injiniya Maikano Ɗan Saurayi da ke Gombe, shi ma duk lokacin da muka nemi taimakon za mu yi wani abu yana tallafa mana. Allah ya saka musu da alheri.
Wanne tallafi ko gudunmawa ƙungiyar ki ta ke buƙata daga gwamnati, ƙungiyoyi masu ba da tallafi da sauran jama’a masu hali?
To, a gaskiya duk wanda ya san ayyukan ƙungiya, musamman irin namu na ba da tallafi da ayyukan jin ƙai, ya san ba a iya tafiyar da komai sai da kuɗi, ga shi mu ba masu kuɗi ba ne. Da ni da sauran abokan tafiyar tawa duk ba masu ƙarfi ba ne, sai dai rufin asiri. A haka ka ke yin taka ɗawainiyar kuma ka ke yin ta wani. Idan da so samu ne a ce a samu wasu masu hali, ko hukumomin gwamnati su amince a riqa tallafa mana da jari ko kayan sana’o’in da za a raba wa matan da suka koyi sana’a a ƙarƙashin ƙungiyar mu, don su iya riƙe kansu.
Ko kuma idan mun ɓullo da wani shiri na taimakawa al’umma a ce gwamnati ko wani mai hali ya karva don ɗaukar nauyin waɗanda shirin zai amfanar to, babu shakka za mu cimma nasara sosai, kuma za a rage ƙuncin talauci, da zaman banza, da ke sanadin fitintinu iri iri a ƙasar nan.
Yanzu lokaci ne na kakar siyasa da ‘yan siyasa ke jawo ƙungiyoyi irin naku domin kusantar jama’a da ba da tallafi, kun samu irin wannan damar ku ma?
To, a gaskiya har yanzu dai abin bai zo ta kan mu ba. Babu irin ƙoƙarin da ba mu yi ba na isa ga irin waɗannan ‘yan siyasa, don samun damar su zo su tallafawa matan da muke koyawa sana’o’i da masu fama da ƙuncin rayuwa, da marayu maza da mata, amma abin ya garara.
Ko da mun yi dacen ganin su mun gabatar musu da buƙatar mu, sai dai a ce za a yi wani abu, amma babu abin da ake yi, sai yaudara da rashin cika alƙawari. Sai dai har yanzu ƙofar mu a buɗe ta ke, ba mu sani ba, ko waɗannan sabbin ‘yan siyasa masu zuwa za su bambanta da sauran.
Yaya ki ke kallon rayuwar ƙunci da wasu mata zawarawa da waɗanda mazajen su na aure suka rasu suke yi, da yadda ya kamata al’umma ta riƙa tallafa musu?
Wannan haka ya ke, babu shakka mata zawarawa da suka rasa mazajen aure na rayuwa cikin wani mawuyacin hali na rashin taimako da kulawa, saboda da halin rayuwar da ake ciki, ‘yan uwa ko dangi ba sa iya jure taimakawa, ballantana dangin miji, da ba kasafai suke iya kula da ‘ya’yan marayun da aka bari ba. Ni ma na shiga irin wannan rayuwar na kuma san zafin ta. Ni kaina, Allah ne ya kawo min wani mutum da na bai wa magani ya ji daɗi, ya ba ni tallafin babur mai ƙafa uku na Keke Napep, don in riƙa bayar da haya ina samun abin da zan ciyar da yarana. Wannan shi ya taimake ni na iya tsare mutuncina da na iyalina, ba mu tagayyara mun shiga halin bara ko roƙe-roƙe ba.
Amma ba kowacce mace ce ke samun wannan damar ba, babu wata rana da ba za ka ga wata ta zo gidana neman taimako kan abin da za a ci ba. Ga matsalolin na cin zarafi da rashin kula daga matan da suke da aure, waɗanda mazajen su ba sa tausaya musu. Wani lokaci kuma matan ne suke wulaƙanta mazajen da raina samunsu. Akwai mutumin da ya kawo min ƙorafin matarsa tana dukansa har ya nuna min shatar bulala a jikin sa, saboda yadda ta ke cin zarafin sa, amma babu yadda zai fito ya faɗi abin da ke faruwa da shi, saboda kasancewarsa namiji. Ban tava girgiza ko in karaya sanadiyyar halin da na ke ciki ko ya sanyaya min gwiwa a kan rashin samun tallafi da ba ma yi.
Wacce nasiha ki ke da ita ga ma’aurata, musamman duba da irin ƙuncin da ake ciki?
To, Alhamdulillahi. Gaskiya ana cikin wani hali na ƙuncin rayuwa. Mata suna fuskantar ƙalubale mai yawa a gidajen aure, saboda nauyin kula da iyali ya fara komawa kansu, wasu mazajen ba sa yi musu adalci wajen kyautatawa. Ina samun ƙorafe-ƙorafe iri-iri daga mata da ke neman yadda za a share musu hawaye. Kuma rashin samun inda za su kai kukan su shi yake sa wasu matan shiga fasiƙanci da zubar da qimarsu, don su samu abin da za su ci. Gaskiya ya kamata mazaje su riqa duba haɗarin da suke jefa matansu da yaransu a ciki.
Ni wanda ya taimaka min da shawarwarin yadda zan tallafi rayuwar iyalina bayan jarrabawar da na fuskanta, namiji ne aminin maigidana ne. Kuma shi ya ƙarfafa min gwiwa kan kada na bari yarana su tagayyara ko su rasa ilimi, ko da kuwa sai na sayar da sutura ta ne. Alhamdulillah, ga shi yanzu duk ya wuce, yara sun girma kuma sun yi karatu daidai gwargwado, ni ma su ne suke koya min wasu abubuwan.
Wacce gudunmawa za ki iya cewa kin samu daga abokan hulɗarki Kirista, wajen gina wannan ƙungiya?
Gaskiya Kirista na daga cikin waɗanda suka taimakawa cigaban wannan ƙungiya. A baya na gaya maka yadda wani bawan Allah Kirista, Rabaran Hussaini Gotom ya ba ni shawarar mayar da kwamitin mu na Mauludi zuwa ƙungiya mai zaman kanta, kuma har yanzu duk lokacin da wata dama ta samu ta ba da tallafi, ko wata shawara ba ya ƙasa a gwiwa zai kira ni ko ya zo har gidana mu yi magana da shi. Akwai irin su Pastor Benji da sauransu. Hatta a cikin shugabannin ƙungiya muna da Kirista da komai tare da su muke yi.
Ba a jima ba ma da Babban Sakataren Hukumar Kula da Jigilar Maniyyatan Kirista masu zuwa ziyarar ibada, Rabaran Yakubu Pam, ya gayyaci ƙungiyar zuwa taron haɗin kai da zaman lafiya, kuma ƙungiyar Hablul Mateen ce kaɗai daga ƙungiyoyin Musulmi da aka gayyata. Mun je kuma an karrama mu sosai. Ni na saba da hulɗa da Kirista saboda mun taso tare a unguwar bayan Chwel Yep a Nasarawa Gwong, kuma muna girmama juna ba tare da nuna musu ƙyama ko wariya ba.
Yaya alaƙar ƙungiyar ki da sauran ƙungiyoyi irin naku a nan Jos?
Muna da kyakkyawar alaƙa da su sosai, muna ayyuka na haɗin gwiwa, kuma a kan gayyace mu idan wani taro ya taso, mu ma kuma muna gayyatarsu. Muna cikin ƙungiyoyin haɗin gwiwar Gamayyar Ƙungiyoyin Mata Musulmi ta FOMWAN a Jihar Filato, akwai kuma sauran ƙungiyoyi da dama da muke aiki tare, a duk lokacin da dama ta samu.
Wanne ƙalubale ki ke fuskanta wajen tafiyar da wannan ƙungiya?
To, babu shakka babu wata tafiya ta jama’a da za a yi ba tare da fuskantar ƙalubale ba. Akwai ƙalubale na rashin samun kyakykyawar fahimta wani lokaci da wasu mambobi, musamman waɗanda wani lokaci za su nemi shiga ƙungiya da tunanin ana samun kuɗi a ciki, ko kuma idan sun ji wani ya yi alƙawarin zai taimakawa ƙungiyar da wani abu, idan sun ji shiru sai su riƙa tunanin ko an bayar ne ba a ba su komai ba.
Dalili kenan da na ke bayyana rashin jin daɗina da yaudarar da wasu ‘yan siyasa ko masu hannu da shuni ke yi wa ƙungiyoyi irin namu, suna haɗa su rigima da mambobin su da jama’ar gari. Sai mutum ya zo taro kana yi masa kallon babban mutum, amma sai ya zo ya yi ta alƙawari na yaudara, da ƙyar ya iya baku wani abu, jama’a kuma su riqa tunanin kuna samun wani abu.
Wacce karin magana ce ta ke tasiri a rayuwarki?
Na fi ganin dacewar a ce Mai Kamar Zuwa Kan Aika, amma wajen da Bahaushe ke cewa, Kowa Ya Ce Zai Baka Riga Kalli ta Wuyansa, bai yi min daidai ba, domin kuwa sau da dama waɗanda ke yin abin alheri ko bajinta, idan ka kalle su ba su da wannan kamar, sai dai kyakkyawar zuciya. Su masu kyakkyawar riga ta alfarma akasari duk holoƙo ne!
Na gode.
Ni ma na gode sosai.