Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Ali Madakin Gini ya bayyana cewa abin dariya ne a ce waɗanda ba ‘yan jam’iyyar NNPP ba su yi yunƙurin cire shi daga muƙaminsa.
A wata tattaunawa da jaridar Daily Nigerian, Madaki ya zargi jagoran NNPP na ƙasa, Rabi’u Kwankwaso da kitsa yunƙurin tsige shi da ga muƙamin na sa.
A cewarsa, ya za a yi waɗanda shugabancin jam’iyya na ƙasa ya kora su samu ikon cire wani daga muƙaminsa, inda ya ƙara da cewa wani yunƙuri ne na wasu da su ke rawa da bazar Kwankwaso “kuma su ke ganin cewa duk abinda ya faɗa ta zauna.”
“Waɗanda su ka rattaɓa hannu a takardar ba ‘yan jam’iyyar NNPP ba ne. Kwanan nan kotu ta kori shugabancin jam’iyar ɓangaren Kwankwaso.
“Saboda haka wannan su na ɓata wa kan su lokaci ne kawai saboda kwanan nan kotu to kori shi kansa Kwankwason daga jam’iyyar. Amma ka san dole su riƙa rawa da bazar Kwankwaso,” inji Madaki.