Abin tausayi irin na George Floyd da ya riƙa wakana a Amurka abin kunya ne gare ta

Daga CMG HAUSA

Kwanan baya, wakilin ƙasar Sin ya bayyana matuƙar damuwa a yayin taron majalisar kare haƙƙin ɗan Adam ta MƊD karo na 51 dangane da yadda hukumomi masu ruwa da tsaki na ƙasar Amurka da wasu ƙasashe suke nuna wa ‘yan ƙananan ƙabilun bambanci yayin da suke aiwatar da doka, ya kuma buƙace su da kalli kansu yadda ya kamata dangane da mummunar matsalar wariyar launin fata da nuna bambanci tsakanin ƙabilu, su aiwatar da sanarwa da tsarin ayyuka na Durban, a ƙoƙarin kauce wa sake abkuwar abin tausayi da ya wakana kan George Floyd.

Shekara guda bayan mutuwar George Floyd, ‘yan sandan Amurka sun kashe ‘yan asalin Afirka a ƙalla 229, lamarin da ya sake bayyana rashin gaskiyar Amurka ta fannin kare haƙƙin ɗan Adam.

Amurka, ƙasa ce da ba a tabbatar da babban haƙƙin ɗan Adam na rayuwa, kuma babu demokuraɗiyya ko kaɗan.

A watan Agustan bana, kwamitin yaƙi da wariyar launin fata na MƊD ya soki Amurka kan batun nuna wariyar launin fata da ya daɗe yana addabar Amurka, yayin da yake duba yadda Amurka take aiwatar da yarjejeniya mai ruwa da tsaki.

Kana kuma, a yayin taron majalisar kare haƙƙin ɗan Adam ta MƊD karo na 51 da ake gudanarwa, mahalarta taron sun bukaci Amurka da ta ɗauki tsauraran matakai don kawar da wariyar launin fata a ƙasar baki ɗaya.

Bai kamata Amurka ta kau da kai daga sukan da ƙasashen duniya ke yi mata ba.

Ya dace ta saurari wannan batu da idon basira, ta fara kyautata halin da ake ciki a cikin gidanta a fannin kiyaye haƙƙin ɗan Adam, ta duba ta kuma yi gyara kan dokoki, manufofi da matakai masu nasaba da wariyar launin fata a cikin gida, ta bi bahasin batutuwan cin zarafi da ‘yan sandan ƙasar suka aikata, ta aiwatar da doka kan masu cin zarafin da kuma biyan diyya ga waɗanda aka ci zarafin nasu.

Mai fassara: Tasallah Yuan