Abinda ke jawo yawaitar ficewar kamfanonin mai na ƙasar waje daga Nijeriya (2) – Sani Ɓaɓura

Daga AMINA YUSUF ALI

Komai na tafiya daidai wajen haqo mai a Nijeriya har wajen ƙarshan 1980 zuwa farkon 1990 lokachin da guraren haƙar man suka fara fuskantar matsaloli kamar haka:

Guraren ƙauyuka ne futuk, babu ruwan sha mai tsafta, ba wutar lantarki, gidajensu na bukka ne a kan ruwa suke kwana, suke bahaya, makarantun ‘ya’yansu ginin ƙasa ne, rufin ciyayi; kuma duk lokacin da bututun dake ɗauke da mai ya fashe, sana’arsu ta kamun kifi da noma ta  shiga uku. Hakazalika, sai sun yi tafiya a kwale-kwale mai nisa kafin su sami ruwan da za su sha.

Ƙauyukan kuwa da Turawan suke, yadda ka san Dubai suke ko Paris ko Landan. Ga lantarki ba ɗaukewa ko dare ko rana. Ga gidajensu da makarantun yaransu da guraren shaƙatawarsu masu kyau.

Wannan yanayi ya janyo zanga-zanga daga ƙungiyoyin kare muhalli wanda marigayi Ken Sarowiwa ya jagoranta. Sai da suka fara kashe wasu daga cikin sarakuna ‘yan kanzagin turawa sannan suka kai kokensu ga Majalisar Ɗinkin Duniya suka shiga cikin masu zanga-zangar siyasa ta 12 ga watan Yunin shekarar 1993. Hakan dai ta kai a zamanin mulkin Sani Abacha shari’a ta kashe su.

Kashe su ya janyo sanya takunkumin karya tattalin arzikin ƙasa ga gwamnatin Abacha, har ma daga ƙarshe aka kashe shi Abachan da M.K.O. Abiola. Bayan kashe Abiola da Abacha, yankin Neja Delta ya zauna lafiya har zaɓen 1999.

‘Yan siyasa don biɗar mulki sun yi amfani da ‘yan ta’adda wajen yaƙin neman zaɓe ta hanyar ba su kuɗaɗe, makamai da muggan ƙwayoyi.

Bayan cin zaɓen 1999, daga nan ‘yan ta’addan suka riƙa amfani da makamansu wajen yaƙar junansu.

Waɗanda suka yi nasarar zaɓe idan suka rinƙa yaƙar gwamnati idan ba su sami abinda suka nema ba, ga kuma gaba tsakaninsu da abokan hamayyarsu.

Gwamnoninsu irin su Peter Odili, James Ibori da D.S.P Alamiesegha suka yi nasarar samun ƙarin kason kuɗin mai (Derivation) daga kashi 3% zuwa kashi 13%, a zamanin da farashin gangar mai ke ƙaruwa.

Ganin kuɗin da ake samu wanda sau tari talakawan su ba amfanuwa suke ba, da kuma burin ‘yan siyasa na sai sun zarce kan karagar mulkin da suke kai ko kuma a ƙwaci mulkin da ƙarfin tsiya. ‘Yan ta’adda irin su:

1.Movement for the Emancipation of Niger Delta ƙarƙashin Tompolo.

  1. Niger Delta People’s Volunteer Force ƙarƙashin Mujaheed Asari Dokubo.
  2. New Delta Avengers
  3. Niger Delta Liberation Front.
  4. Niger Delta Marine Force. 
    da sauransu ƙarƙashin su Tom Ateke, Henry Orkah suka yunƙuro.Banda maganin ‘yan adawa, aikin su shi ne:
  5. fasa bututun mai a saci man. A da can ma hukumomi na ruwaitowa ana satar man Nijeriya ganga 200,000 zuwa sama a kullum. Yanzu waɗannan alƙalumma sun ninninka.
  6. Kama Turawan dake aikin hakar mai a yi garkuwa da su domin biyan kuɗin fansa.
  7. Ɓata muhalli a dalilin fasa bututun mai da ake yi wanda ke haifar da kashe maƙudan kuɗaɗe ga manyan kamfanikkan mai ke yi wajen gyara gurin. 
  8. Kai kamfanikkan mai ƙara a kotuna a kan laifin ɓata ruwa da gonaki, bayan ba su ne suka fasa bututun man ba, maƙarƙashiya ake musu, kuma a ci su tarar maƙudan kuɗaɗe.Mu kwana a nan.

Alhaji Sani Ya’u Ɓaɓura masani kuma mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum.