Abinda ya jawo matsalar ƙarancin fetur a Nijeriya da maganinsa – Korie

Daga AMINA YUSUF ALI

Shugaban ƙungiyar masu samar da man fetur da gas (NOGASA), Bennet Korie ya yi gargaɗin cewa, kasuwanci zai iya gagarar mutane da dama matuƙar za a cigaba da sayar da baƙin mai a kan farashin Naira 850 kowacce lita.

Ya ƙara da cewa, baban dalilin da ya sa aka samu tashin farashin mai shi ne tashin farashin baƙin mai na yankin mai masu jigilar kai mai zuwa Abuja su ne Ummul aba’isin na tashin farashin man fetur a birnin Tarayyar da ma ƙasar bakiɗaya.

Ya bayyana haka ne a wata zantawarsa da manema labarai ranar Talatar da ta gabata a Abuja. Shugaban na NOGASA ya ƙara da cewa, ba don matakan gaggawa da aka ɗauka na tsayar da abin ba, da matsalar ƙarancin mai ta cigaba da ta’azzara fiye da yadda take a yanzu a faɗin ƙasar nan.

A don haka ya ce, ya kamata gwamnatin ta yi wani abu da gaggawa kafin farashin baƙin mai ya yi tashin gwauron zabi wanda ake ganin zai iya kai wa har Naira 1000 kowacce lita.

Hakazalika a cewar sa, yaƙin Rasha da Yukiren shi ma ya taimaka wajen tashin farashin man fetur a Duniya, abinda ya shafi har da Nijeriya.

Idan ba a manta ba, da ma tun a watan Fabrairun shekarar nan ta 2022 aka sha fama da matsalar ƙaranci da tashin farashin man fetur. Hakan ya jawo dogayen layuka a gidajen mai a faɗin ƙasar nan. Kuma abin ya faskara magancewa, duk kuwa da matakan da ake ɗauka wajen magance shi ɗin.

Sai dai a cewar Korie, mafita ita ce kawai gwamnatin Tarayya ta ƙara farashin mai a gidajen mayuka bayan ta cire tallafin mai da take kwashe maƙudan kuɗaɗe daga Baitul Mali ƙasar nan take biya a kowacce shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *