Abinda ya sa APC ta ɗage sayar da fom ɗin takara a jam’iyyar

Daga AMINA YUSUF ALI

A yanzu haka dai jam’iyyar APC ta ɗage sayar da fom ga masu sha’awar takara a jam’iyyar, kuma ta tura daraktocinta zuwa ‘hutun dole’.

Wannan lamari dai ya zo a ba-zata domin al’umma sun kasa kunnuwa kuma sun buɗe idanun don ganin yadda za ta kaya ganin yadda aka ba da sanarwar sayar da fama-faman takarar jam’iyyar a ranar Asabar, 23 ga watan Afrilu, 2022. Musamman saboda yadda sanarwar ta ja hankalin mutane saboda yadda mutane suke kukan an tsawwala farashinsu.

Amma sai kwatsam! Aka ji sanarwar an ɗage sayar da fom ɗin nuna sha’awar tsayawa takara a jam’iyar.

Hakazalika jam’iyyar ta soma garambawul ga tsarin shugabancin babban reshenta na qasa bakiɗaya, inda suka umarci daraktocin Jam’iyyar guda shida su tafi hutun dole.

Waɗannan bayanai suna ƙunshe ne a wata takarda wacce take ɗauke da kwanan watan ranar 21 ga Afrilu, 2022 kuma da sa hannun Makatakardar Jam’iyyar APC na ƙasa, Otunba Iyiola Omisore. A cikin takardar ne ake umartar daraktocinta na ƙasa da su tafi hutu sannan su damƙa ayyukan ofishinsu ga shugabanninsu na sassan da suke.

Dama tun a ranar Larabar da ta gabata ne dai Kwamitin zartarwa na APC na ƙasa, shi ya ba da umarnin a fara sayar da Fom ɗin takarar jam’iyyar a ranar Asabar ɗin.

Amma wata majiya da mai tushe ta bayyana wa Blueprint cewa, abinda ya jawo aka fasa sayar da fom ɗin shi ne, tsaikon da aka samu daga ɗan kwangilar da zai buga fom ɗin ne. An samu tasgaro bai kawo a kan lokaci ba.

Wata majiiyar kuma ta bayyana cewa, abinda ya hana a fara sayar da fom ɗin shi ne, jam’iyyar APC har yanzu ta kasa samun cimma matsaya guda a kan irin dokokin sayar da fom ɗin da kuma ranar da za a yi zaɓen fidda gwani na cikin gida.

A halin yanzu dai ba wata rana tsayayya da aka tsayar don cigaba da sayar da fom ɗin har yanzu dai ana jiran ji ta bakin kwamitin NWC. Kamar yadda majiyar ta cigaba da cewa.

Domin a cewar majiyar, ɗagewar ya zama dole saboda tazgaro da aka samu daga ɗan kwangilar na ƙin cika alqawari ya buga fom ɗin kuma ya kawo su a cikin ƙarshen makon.

Sannan kuma tsare-tsaren da ake yi a jam’iyyar shi ma gyara ake yi da ya sa dole daraktocin su ɗan tafi hutu domin a samu sararin gudanar da gyaran. Kuma a cewar majiyar ma, bayan daraktocin, an ba wa shugaban sashen Shari’a na APC shi ma umarnin tafiya hutun dole

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *