Abinda ya sa Asusun Tarayya zai raba kuɗin ƙananan hukumomi na Janairu ga jihohi

Daga BELLO A. BABAJI

A halin yanzu Kwamitin Asusun Tarayya (FAAC) bai kai ga biyan kuɗin wata-wata kai-tsaye ga ƙananan hukumomi 774 na Nijeriya ba, tun bayan ƴancin cin gashin kai da Kotun Ƙoli ta ba su a shekarar 2024.

A jiya Alhamis ne aka gano cewa wa’adin da aka bai wa ƙananan hukumomin na su bada bayanan asusun bankuna ya cika.

Wata majiya ta ce za a bai wa ƙananan hukumomin kuɗaɗensu ne ta hannun gwamnatocin jihohinsu.

Majiyar ta ce za a bai wa Hukumar Ilimi na bai-ɗaya (UBEC) da rassan Cibiyar Kiwon lafiya (PHC) kuɗaɗensu kai-tsaye daga Asusun Tarayya.

Saboda rashin bin ƙa’idar na wa’adin da aka bayar don su miƙa asusun da za a saka kuɗaɗen ga ƙananan hukumomin ya sa za a bayar ta jihohinsu.

Tuni dai Asusun Tarayyar ya saki Naira biliyan 860.252 ga gwamnatocin jihohi wanda a ciki, biliyan N498.498 nasu ne, yayin da kuma biliyan N361.754 na ƙananan hukumomin ne.

Haka kuma wani jami’in FAAC da ya nemi a sakaya sunansa ya ce Asusun ya tura kuɗin ga jihohin saboda ƙananan hukumomin ba su cike ƙa’idodin da aka ba su ba na samun kuɗin kai-tsaye.