
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamna Chukwuma Soludo na Anambra, ya ce gwamnatinsa ta janye daga yarjejeniyar karɓar Aron kuɗi ne daga Bankin Duniya don tsaratar da jihar daga faɗa wa matsanancin bashi.
Ya bayyana haka ne ga tawagar yaɗa labarai na marigayi tsohon gwamnan jihar, Sanata Ifeanyi Uba a lokacin da suka je ziyarar gani da ido na ayyukan gidan gwamnatin jihar da na masaukinta a Akwa, ranar Lahadi.
Ya ce, ba iya bashin wani banki ba, har ma wanda Gwamnatin Tarayya ta yi wa gwamnatocin jihohi tayi a shekarar 2024 ba su karɓa ba.
Gwamna Soludo ya ce gwamnatinsa ta duƙufa ne wajen kammala ayyukan al’umma a jihar, waɗanda da dama ana gab da gama su.
Ya ƙara da cewa, Anambra ita ce kaɗai jihar da ta ƙi karɓar bashin Bankin Duniya wanda tun kafin ya hau mulki aka rattaɓa wa hannu, ya na mai cewa ya yi la’akari ne da sharuɗɗansa da ƙalubalen da karɓar sa ka iya haifarwa a nan gaba.
Har’ilayau, Soludo ya ce wannan shi ne karo na farko da jihar za ta samu gidan gwamnati na dindindin tun tsawon shekaru 34 da kafa ta.
Bugu da ƙari, ya ce gwamnatinsa tana aikin titina da tsawonsu ya kai kimanin kilomita 750, inda a yanzu an kammala ɓangaren kilomita 410 wanda a tarihin jihar ba a taɓa samun irin haka ba.