Abinda yake hana ƙauna tasiri a auren dole duk daɗewarsa

Daga AMINA YUSUF ALI

Barkanmu da sake haɗuwa a wani makon a jaridarmu mai farin jini ta Blueprint Manhaja. A wannan mako za mu tattauna a kan dalilan da suke sanya a yi auren dole kuma duk da an ɗauki lokaci mai tsawo a cikinsa, ƙauna ba ta shigowa ta yi tasiri. Domin sai ka ga namiji ya yi shekaru masu yawa da macen da aka yi musu auren dole, ko auren haɗi, amma sai ka ga bayan shekaru ya dage sai ya ƙara aure. Ya auri zaɓinsa wace yake so.

Idan ma kenan yana jin kunya ko nauyin iyayenta ko nasa ya hana ya sake ta. Haka mace ita ma tana daɗewa da namijin da aka yi mata auren dole, tana iya shafe shekaru da mutum ba tare da ta so shi ba. Ko da sun tara yara, ita dai kawai ba za ta tava sonsa ba. Kuma kunyar iyaye da ganin girmansu galibi yake sa ta yi biyayya ta zauna. Amma me yake kawo haka? Za ku ji Insha’Allah a wannan rubutu. A sha karatu lafiya.

Menene auren dole/auren haɗi?

Auren dole wani aure ne wanda iyaye nasu alaƙa da juna suke haɗawa tsakanin yaransu maza da mata ba tare da yaran suna soyayya ba ko kuma sun shawarci yaran ba. A ƙasar Hausa wani lokacin ma iyayen yaran ba su san iyaye maza sun ƙulla waccan maganar ta haɗa yaransu aure ba ballantana yaransu da suke ganin su suka haife su, kuma suna da iko a kansu. Auren haɗi zai iya zama na zumunci, ko wata alaƙa ta abota, ko kuma haka kawai.

Dalilan da suke sa wa iyaye suke haɗa yaransu aure?

Akwai dalilai da dama da suke sa iyaye su haɗa yaransu aure da abokan zaman da ba soyayya a tsakaninsu waɗanda suka haɗa da:

*Iyaye kan haɗa aure domin a ƙara ƙarfafa zumunci tsakanin dangi ko abokai. Wani kuma kunya ce a tsakani. Idan ya nemi aure dole a ba shi saboda ƙarfafa wannan alaƙa tasu. Ko da yarinyar ba shi take so a samarinta ba.

*Iyaye kan haɗa aure saboda suna ganin ɗansa/ko ‘yarsu ba su da wayewa ko gogewar da za su samar wa kansu abokan zaman da suka dace da su. Wato mai nagarta wanda su iyayen suke ganin shi ya cancanta su haɗa zuriyya da shi. Musamman idan suna ganin yaran nasu suna ƙoƙarin zaɓin abinda bai dace ba.

*Ruwan idon yara su kasa zaɓen aboki/abokiyar rayuwa nagari. Sai iyaye su raba gardama su zaɓi wani ko wata kawai su haɗa shi aure da su.

*Wata manufa ko ta ƙulla alaƙa don kwaɗayin abin duniya ko mulki ko siyasa, da sauransu. Ko da yaran ba sa so, ana haɗa auren saboda su iyayen su cimma wannan manufa/manufofi.

*Idan yarinya mace ta rasa tsayayyen manemi kuma ga shi tana ta ƙara girma shekaru suna gaba, wasu lokutan iyaye kan ba da ita sadaka ko su haɗa ta aure da wani abokin hulda ko dangi. Akwai masu zuwa ma masallatai su ba da hotunna yaransu mata don a zo a nemi aurensu. Kuma duk wanda ya taya, idan sun aminta da shi, za su iya ba shi ko da yarinyar ba ta so.

  • Ana ba da yarinya aure fisabilillahi, idan Uba ya yaba da hankalin wani ko a cikin unguwa ko wani waje kuma yake ganin zai iya haɗa zuriyya da shi, yakan iya haɗa shi aure da ‘yarsa don kwaɗayin nagartarsa.

*Ra’ayi ma yana sa a yi auren dole. Wani Uban ba ya jira yaransa mata su kai shekarun da ya kamata su fara taɗi da samari, suna zuwa 13 ko sha huɗu za su yi farat su ba wa wanda suka amince wa aure.

Wannan kaɗan daga dalilan da suke sa wa a yi auren dole/auren haɗi kenan.

Illolin auren dole

  • Yana cutar da zuciyoyin ma’aurata, domin auren wanda ba ka so, sai ka daure kake iya kyautata masa. Saboda so sinadari ne wanda yake ginshiƙin aure. Duk da dai ba so ne yake riƙe aure dukkansa ba, amma yana da tasiri mai yawa. Ba lallai ne su samu jituwarsu ta zo ɗaya ba. Sai an dace kafin a samu a fahimci juna. Hakan kuma na iya kai wa ga rabuwar aure. Haka wani lokacin auren dole kan zama mafarin shaiɗan ya yi nasara a yarinya ta kashe kanta, ko ta gudu ta bar iyayenta ta shiga Duniya, ko kuma ta yarda da auren, amma a gidan mijin tana cigaba da alaƙa da wanda take so ɗin. Ko kuma ta yi ta rashin mutunci har ya gaji ya sallame ta.

Me yake kawo tangarɗar zama a auren haɗi/auren dole?

Gaskiya a zamanin da ba a san wani abu wai shi auren soyayya ba. Abinda aka sani shi ne, auren haɗi. Iyaye su suke zaɓar wa yaransu abokan aure. Kuma akan zauna lafiya ƙalau da girmama juna. Amma a wannan zamani auren soyayya ma ya aka ƙare, balle na haɗi? Abubuwan da suke jawo tangarɗar zamantakewa a auren dole kuwa, sun haɗa da:

  • Ɗabi’ar ɗan adam ta rashin son a tursasa shi, da ma tana nan. Shi mutum ya fi son ya yi abu bisa ra’in kansa ba ya son a tursasa shi. Idan aka yi wa mutum aure da wanda/wadda ba ya so, a ɗabi’arsa yakan yi ƙoƙarin bijirewa. Wannan bijirewar kuma takan kawo hatsaniya a zamantakewa ta auren.

*Rashin kyautatawa musamman daga ɓangaren miji: Wasu lokuta namiji yakan fi mace sauƙi ra’ayi game da ƙiyayya. Zuciyarsa ta fi saurin sakkowa. Ta mace ma tana iya saukowa, ko ba ta son mutun ta so shi saboda kyautatawa. Amma wasu mazan sun riga sun san cewa, matar nan da suka aura ba sonsu take tun da fari ba, maimakon su dinga kyautata mata ba don komai ba ma, don su samu kwanciyar hankali a gidansu, sai ka ga ya ɓuge da biye mata wajen nuna tawaye a kan rashin sonsa. Kuma hakan wani mabuɗi ne na ta’azzara ƙiyayyar juna da rashin zaman lafiya. Da ma yaya lafiyar kura…?

  • Ɗaukar fansar namiji: Wasu matan kan yi kuskure nuna ƙiyayya ƙarara ga mijin da ake son haɗa su aure. Wa ya aike ki? Idan ba ki haɗu da azzalumi da zai je ya buga Miki sihiri ba, to za ki haɗu da wanda zai ce shi kuma ko ana ha-maza, ha-mata sai ya aure ki don ya rama wulaƙancin da aka yi masa. Irin wannan sai ya ga mace ta shigo hannu sai ya shiga gallaza mata ta hanyoyi kala-kala, kuma shi ba zai sake ta ba.

Irin wannan ko shekara nawa suka yi, kuma ko yara nawa suka yi, za ka ga ba za ta tava sonsa ko tausayi sa ba. Kawai za ta zauna ne saboda biyayyar iyaye kuma da neman aljannarta. Wata kuma sam ma ba ta iya yi masa biyayyar saboda tsananin ƙiyayya.

Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce: ” An gina zuciya akan abin biyu, ta so mai kyautata mata, ta kuma ƙi mai ƙuntata mata. To in dai ba ka kyautata wa matarka, a ɗabi’ance, dole ƙiyayarka ta cika mata zuciya. A nan za mu dakata, sai wani makon idan rai ya kai, za mu cigaba. Nagode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *