Abokai na zahiri suna zurfafa hulɗar zumunci a sabon zamani

Daga CMG HAUSA

Jiya Jumma’a ne babban sakataren kwamitin ƙolin JKS kuma shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya yi shawarwari da takwaransa na ƙasar Cuba Miguel Díaz-Canel wanda ke ziyarar aiki a ƙasar Sin, inda suka amince cewa, za su ci gaba da ƙara ƙarfafa jagorancin siyasa kan hulɗar jam’iyyunsu da ma ƙasashe biyu, tare kuma da ci gaba da ƙara zurfafa hulɗar zumunci ta musamman dake tsakanin Sin da Cuba a sabon zamanin da ake ciki.

Duk da cewa, ƙasashen biyu na da nisa a tsakaninsu, amma hulɗar dake tsakaninsu tana da kyau ƙwarai, kuma Díaz-Canel, shi ne shugaba na farko daga nahiyar Latin Amurka da ya kawo ziyara ƙasar Sin, bayan babban taron wakilan JKS karo na 20, lamarin da ya nuna cewa, hulɗar dake tsakanin Sin da Cuba ta kasance abin koyi ga ƙasashe masu bin tsarin gurguzu da ƙasashe masu tasowa yayin da suke ƙoƙarin taimakawa juna.

Yayin tattaunawar ta su, shugaba Xi ya waiwayi zumuncin dake tsakanin Sin da Cuba, shugaba Díaz-Canel shi ma ya bayyana cewa, ƙasarsa tana mai da hankali matuka kan hulɗarta da ƙasar Sin, duk waɗannan sun nuna cewa, sassan biyu suna darajanta daɗaɗɗen zumuncin dake tsakaninsu.

Ko shakka babu ziyarar shugaban ƙolin Cuba a kasar Sin, za ta ƙara haɓaka haɗin gwiwar dake tsakanin sassan biyu.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa