Abubuwan da za su taimaka wajen inganta zaɓen 2023 – Dambazau

Daga BASHIR ISAH

An bayyana cewa, tsarin karɓa-karɓa zai taka rawa gaya wajen inganta zaɓuɓɓukan 2023.

Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Laftanar-Janar Abdulrahman Dambazau ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wajen Taron Lacca na 2021 da kamfanin Blueprint ya shirya ranar Talata Abuja.

Kazalika, Dambazau ya ce sake fasalin ƙasa gami da sha’anin addini na daga cikin abubuwan da idan aka riƙe su za su yi tasiri mai ma’ana ga babban zaɓen na 2023.

Ya ƙara da cewa, tun bayan samun ‘yancin kai, Nijeriyar ta gudanar da manyan zaɓuɓɓuka guda shida, wanda idan Allah Ya so za ta shaida na bakwai baɗi.

Daga nan, tsohon Ministan ya buƙaci ‘yan Nijeriya da a maida hankali sosai wajen yaƙi da talauci da bunƙasa fannin kiwon lafiya da dai sauransu don inganta rayuwar ‘yan ƙasa