Abuja: An yi jana’izar mayaƙan sama da suka rasu a haɗarin jirgin sama

Daga BASHIR ISAH

An gudanar da jana’izar jami’an sojin saman nan su 7 da suka rasu a haɗarin jirgin sama da ya auku a Abuja a Lahadin da ta gabata.

Jami’an da lamarin ya shafa sun cim ma ajalinsu ne bayan da jirginsu, ƙirar Beechcraft King Air 350, ya faɗo a ƙauyen Bassa daura da Babban Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe, bayan da suka tashi da nufin zuwa aiki a jihar Neja.

Mai Magana da Yawun Rundunar Sojin Sama na Nijeriya, Air Vice Marshal Ibikunle Daramola ya ce jirgin ya fuskanci matsalar inji kafin aukuwar haɗarin.

Cikin waɗanda suka halarci jana’izar wadda aka gudanar a babbar maƙabartar sojoji da ke Abuja, har da Ministan Tsaro, Bashir Magashi, Shugaban Sojoji, Major General Lucky Irabor, dangin marigayan da dai sauransu.

Sa’ilin da yake magana a wajen jana’izar, Shugaban Rundunar Mayaƙan Sama, Air Vice-Marshal Oladayo Amao, ya yi kira ga mayaƙan rundunar da su kasance masu ƙwazo a fagen yaƙi da ta’addanci domin tabbatar da cewa yinƙurin da marigayan suka yi bai tafi a banza ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *