Abure ya zama Shugaban Jam’iyyar Labour na Ƙasa karo na biyu

Daga BASHIR ISAH

An sake zaɓan Mr Julius Abure, a matsayin Shugaban Jam’iyyar Labour na ƙasa karo na biyu.

Daliget ne suka sake bai wa Abure wannan dama ba tare da hamayya ba.

An zaɓe shi ne duk da hamayya daga ɓangaren Jam’iyyar NLC.

Shugaban babban taron jam’iyyar kuma Mataimakin Gwamnan Jihar Abia, Mr Ikechukwu Emetu, shi ne ya ayyana Abure a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugabancin jam’iyyar wanda ya gudana ranar Laraba a Nnewi, Jihar Anambra.

Kafin wannan lokacin, an kai ruwa rana tsakanin Abure da NLC ƙarƙashin jagorancin leadership Joe Ajaero. Inda NLC ta buƙaci Abure ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar sannan kwamitin riƙo ya shirya zaɓe ba tare da ɓata lokaci ba.