ACCF ta gudanar da babban taron bita

Daga ABUBAKAR M. TAHIR a Haɗeja

Ƙungiyar Cigaban garin Auyo mai Suna ‘Auyo Concerned Citizens Forum’ (ACCF) a Turance, ta gudanar da babban taron shekarar 2021 a ɗakin taron da ke sakatariyar mulki ta ƙaramar hukumar.

Taron wanda aka fara shi ranar Lahadi 26 ga watan Disamba wanda aka ƙarƙare shi 27 ga wata ya samu halartar ɗimbin al’ummar yanki, ’yan siyasa, masu aarauta, ’yan kasuwa dama ’yan bokon garin.

Da farko an gabatar da kasida mai ɗauke da manufofin zauren dama nasarorin ɗaya samu wanda Shugaban Ƙungiyar, Injiniya Garba Adamu ya gabatar.

Cikin jawabin nasa, ya bayyana cewa, sun kafa zauren ne a shekarar 2016 wanda ya zama inuwa ga duk wani mazaunin yankin.

Ya ƙara da cewa, ya zuwa yanzu sun sami nasarar haɗa kan ’ya’yan mambobin ƙungiyar kuma zuwa yanzu sun sami damar isar da sakunansu ga gwamnati kai tsaye.

Shima a nasa jawabin Hakimin Auyo Alhaji Umar Baffa ya nuna matuƙar farin cikinsa kan wannan ƙoƙari na zauren ACCF inda ya ce, suna sa ran zuwa gaba yankin na Auyo sai zama cikin sahun gaba da ake alfahari da su ta fuska ilimi da sauran ɓangarorin rayuwa.

Hakimi Auyo ya kuma buƙaci mambobin ƙungiyar su zama masu haƙuri saboda gudanar da irin wannan tafiya sai an ɗaure a kuma yi don Allah.

Shi ma a nasa jawabin, shugaban ƙaramar hukumar Auyo, Alhaji Muhammad Baffa Shinge ya yi alƙawarin samar wa zauren na ACCF sakateriya a ko ina ne a garin Auyo domin samar da cigaban yankin.

Baffa ya ƙara da cewa, a shirye suke dukkanin gudunmawar da ta dace domin cigaban yankin.

Dayake gabatar da muƙala mai taken ‘Ƙalubalen tsaro da mafitarsa’, ya kawo jerin matsalolin tsaro da suka addabi arewacin ƙasar nan inda ya bayyana cewa hukumar ’yan sanda a shirye take wajen shawo kan matsaloli.

Ya kuma nuna jin daɗinsa kan yadda zaman lafiya ya samu a jihar Jigawa.

Al’ummar da suka halarci wannan babban taro sun nuna jin daɗinsu da irin namijin ƙoƙarin zauren domin samarwa da garin na Auyo mafita me cike da cigaba ta fuskar Zamani.