ACSEA ta ƙaddamar da aikin samar da makamashi mai ɗorewa a Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ranar Talata ne ƙungiyar haɗin kan Afirka don samun ɗorewar makamashi (ACSEA) da ƙungiyar ‘Pan African Climate Justice Alliance’ suka ƙaddamar da wani shirin miƙa wutar lantarki da ya shafi al’umma a Afirka.

Ana gudanar da aikin na tsawon shekaru uku a wasu ƙasashe huɗu da suka haɗa da Kenya, Botswana, Kamaru da Morocco.

Shugaban gudanarwa na ƙungiyar ACSEA a Nijeriya, Dakta Godwin Uyi-Ojo, ya ce, ta hanyar dandalin ACSEA a Nijeriya, za a samar da ingantaccen hanyar samar da wutar lantarki.

Uyi-Ojo ya ce, abu ne mai matuƙar damuwa ganin yadda ƙungiyoyin farar hula ke da ƙarancin faɗa a ji wajen yanke shawara kan canjin makamashi mai ɗorewa.

A cewarsa, akwai buƙatar ƙarfafawa da horar da ƙungiyoyin farar hula don samun ƙarfin faɗa a ji a cikin yanke shawara da kuma tasiri wajen sauya manufofin makamashi don sabunta makamashin.

“Manufar ACSEA ita ce tabbatar da cewa canjin makamashi mai ɗorewa ya faru a cikin ingantacciyar hanyar samun makamashi. Duk da haka, akwai ƙarancin shiga cikin tsarin yanke shawara kan ayyukan makamashi mai sabuntawa.

“Saboda haka, babban abin da aikin ya fi mayar da hankali a kai shi ne inganta samar da makamashin da ake iya sabuntawa a Nijeriya. Gaba ɗaya, samun isasshen makamashi mai tsafta yana kyau saboda yanayin makamashin a halin yanzu.

“Ƙaddamar da aikin ACSEA yana da muhimmanci don magance matsalolin makamashi don ba da damar tsarin makamashi da rarrabawa wanda ke tafiyar da zamantakewar al’umma da kuma inganta makamashin al’umma a duk tsarin,” inji Uyi-Ojo.

Ya ce, ta hanyar tsarin samar da makamashi ne kawai za a iya magance matsalar talauci da kuma warware matsalar makamashi, yayin da ya yi kira da a cigaba da horar da ƙwararrun masana’antu a cikin gida na na’urorin makamashi masu sabuntawa.

Uyi-Ojo ya ce, hakan zai sa ƙaimi ga cigaban fasaha a fannin makamashin da ake sabuntawa da kuma samar da ayyukan yi ta hanyar fasahohin zamani don tabbatar da cewa Afirka ta zama wurin fasahohi iri-iri.

Daraktan tsare-tsare na ACSEA, Eugene Nforngwa, ya ce, aikin zai ƙarfafa rawar da ƙungiyoyin farar hula ke takawa wajen ingantawa da aiwatar da shirye-shiryen miƙa wutar lantarki mai ɗorewa da kuma tasiri wajen raya manufofi a ƙasashen biyar.

Nforngwa ya ce, Afirka ce ta fi kowacce ƙasa samun makamashi a duniya yana mai cewa, samar da makamashi shi ne fifikon siyasa ga gwamnatoci da masu ruwa da tsaki.

A cewarsa, makamashin da ake iya sabuntawa ya kasance mafi kyawun damar cike irin wannan giɓin, tare da rage yawan hayaƙin da ake iya samu daga fannin, ya ƙara da cewa, shirye-shiryen da ake yi a halin yanzu ba su da haɗin kai kuma ba su da fa’ida sosai.

Ahmed Nagode, Darakta Janar na Cibiyar Koyar da Wutar Lantarki ta Nijeriya, ya ce, akwai buƙatar rage hayaƙin iskar gas a lokacin da ake neman hanyoyin da za a iya sabunta makamashin.

Nagode ya ce, ƙungiyoyin jama’a na da rawar da za su taka don ɗorewar hanyoyin makamashi.

A cewarsa, gina sana’o’in hannu a fannin makamashi zai taimaka wajen samar da damarmaki ga matasa.