Adabin Hausawa ba zai manta da Umaru Ɗanjuma ba – Dakta Abu Sabe

*Mutum ne da kowa ke jin daɗin mu’amala da mahaifina, inji ɗan Marigayi Umaru Ɗanjuma

Daga UMAR GARBA a Katsina

A ranar juma’a 29 ga watan Oktoba 2021, Allah ya karvi rayuwar shahararren marubucin littattafai kuma ɗaya daga cikin waɗanda su ka fara wasan kwaikwayo a arewacin Nijeriya wato Alhaji Umaru Ɗanjuma Katsina wanda aka fi sani da Kasagi. Marigayi Umaru Ɗanjuma Katsina ya yi fice ta fannin wasannin kwaikwayo kamar su ‘magana Jari ce’, ‘Ruwan Bagaja’, ‘Kasagi’, ‘Ya’yan Zamani’ da sauran su, ya kuma rubuta littattafai waɗanda su ka zagaya duniya kamar su ‘Kulɓa na Ɓarna’, ‘Ai Ga Irinta Nan’ da dai sauran su. Manhaja ta tattauna da wani babban malamin jami’a mai suna Dakta Bashir Abu Sabe dake Jami’ar Umaru Musa Yar’adua a Katsina a kan tarihin marigayi Umaru Ɗanjuma wato Kasagi da yadda ya aiwatar da wasannin kwaikwayo da rubuce rubucen da ya yi a lokacin da yake raye.

Dakta za mu so ka gabatar da kanka a taƙaice.
Sunana Bashir Abu Sabe daga sashen nazarin harsunan Nijeriya dake jami’ar Umaru Musa Yar’adua a Katsina.

Ko za ka ba mu taƙaitaccen tarihin marigayi Umaru Ɗanjuma Katsina?
Kamar yadda shi marigayin ke bada tarihinsa za mu iya cewa sunansa Umaru Ɗanjuma Katsina amma an fi sanin sa da Kasagi. An haife shi a shekarar 1950 a unguwar Ƙofar Soro dake cikin garin Katsina a Jihar Katsina dake arewacin Nijeriya,ya yi makarantar firamare a Giɗaɗo primary School daga shekarar 1960 zuwa 1972 daga nan sai ya shiga makarantar Sakandaren gwamnati dake nan Katsina daga shekarar 1972 zuwa 1975.

Bayan ya kammala karatun sakandare ya samu damar shiga wata Makarantar gaba da sakandare dake garin Landan a Ƙasar Burtaniya mai suna ‘Film and Television Training School’ a turance kenan, inda ya ƙara gogewa akan shirya wasannin kwaikwayo da shirye shiryen gidan talabijin kasancewar dukkan karatun da ya yi anan gida Nijeriya da ƙasar waje ya fi maida hankali akan irin wannan karatun, saboda Allah ya ba shi basirar rubutawa da kuma shirya wasannin kwaikwayo irin wanda su ke aiwatarwa a gidan talabijin na ƙasa wato NTA Kaduna.

Waɗanne aikace-aikace ne Alhaji Umaru Ɗanjuma ya fara bayan kammala karatunsa?
To Alhaji Umaru Ɗanjuma ya fara aiki ne a ma’aikatar yaɗa labarai dake jihar Arewa ta tsakiya a Kaduna daga shekara ta 1972 zuwa 1978 daga nan kuma ya yi aiki a cibiyar nazarin al’adu ta Nijeriya wadda ke a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria a shekarar 1978. Ya kuma taɓa zama shugaban nazarin al’adun Nijeriya a wannan jami’a dai ta ABU da ke Zaria.

Daga nan sai Kasagi kamar yadda aka fi saninsa Allah ya jiƙansa ya koma Jihar Katsina cikin shekarar 1989 inda gwamnatin jihar ta ba shi muƙamin mataimakin darakta a hukumar raya al’adu ta Jihar Katsina har zuwa 1991.

Kafin rasuwar Alhaji Umaru Ɗanjuma a cikin wannan shekara ta 2021 gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya naɗa shi shugaban hukumar adana kayan tarihi dake Katsina. Wannan shine muƙaman da ya riƙe har zuwa lokacin da Allah ya yi masa rasuwa.

Waɗanne littattafai ne ya rubuta a lokacin rayuwarsa?
To Umaru Ɗanjuma Katsina ya rubuta littattafai waɗansu ma ba a samu damar wallafa wa ba. Waɗanda aka rubuta kuma suka yi fice bayan ‘Kulɓa na Ɓarna’ akwai wani littafi ‘Ai ga irinta Nan’, ‘The Agony Of Justice’ da dai sauran su.
 
Ko za ka yi mana ɗan tsokaci a kan littafin ‘Kulɓa na Ɓarna’?
To littafin ‘Kulɓa na Ɓarna’ littafi ne wanda hukumar dake wallafa littattafai ta arewacin Nijeriya wato NNPC ta wallafa, kuma sunan littafin ai kamar karin magana ne da ake cewa Kulɓa na Ɓarna ana cewa Jaɓa ce, littafi ne dake nuna irin ta’asar da attajirai ke aikatawa a makarantu, ko a makon da ya gabata kafin rasuwar Alhaji Umaru Ɗanjuma na haɗu da shi a wurin wani taro wanda ‘Open arts’ da sauran ƙungiyoyi su ka shirya inda aka karrama shi, Kasagi ya maimaita cewar littafinsa na ‘Kulɓa na Ɓarna’ ya na nuni da wasu manya dake aikata ba daidai ba amma sai ace babu ruwan manya yara ne ke aikatawa, a taƙaice littafin ‘Kulɓa na Ɓarna’ ya na koyar da mu cewar waɗanda ake tsammanin suke aikata laifi ba lallai bane suke aikatawa ɗin.

Saboda muhimmancin littafin ‘Kulɓa na Ɓarna’ har yanzu ana amfani da shi a manhajar koyarwa ta makarantun sakandare, haka nan hukumar dake shirya jarabawar ƙarshe ta kammala karatun sakandare wato WAEC ta na amfani da littafin wurin shiryawa ɗalibai jarabawa, hakan nan jami’o’i da sauran makarantun gaba da sakandare su na yin nazari akan littafin.

Waɗanne wasannin kwaikwayo Umaru Kasagi ya fito ko ya shirya a zamanin da su ke aiwatar da wasannin kwaikwayo a gidan talabijin na NTA?
Koda yake wasannin kwaikwayon da su ke gabatarwa shida Abokan diramarsa a wannan lokacin hukumar gidan talabijin na ƙasa haɗin gwiwa da wasu hukumomi ne ke ɗaukar nauyin shirya su, shi kuma ya rubuta, ya kan fito cikin diramar a mafi akasari, wasu daga cikin wasannin kwaikwayon sun haɗa da, ‘Magana jari ce’, ‘Ruwan bagaja’, ‘Kishiya’, ‘Ya’yan Zamani’, ‘Baƙin Bature’ da sauran su.

Me ya sa ake kiran sa da Kasagi?
Kasagi na Halima ga naka, Kasagi ya na ɗaya daga cikin rawar da marigayi Umaru Ɗanjuma ke takawa a cikin wasannin kwaikwayon da su ke gabatarwa a gidan talabijin na ƙasa wato NTA, saboda haka za a iya cewa ya na ɗaya daga cikin sunayen wasannin da ake nunawa a gidan talabijin inda shi marigayi ke fitowa da sunan Kasagi. Za ka ji har wani kirari ake masa inda ake haɗa sunansa da na matarsa a cikin diramarsu sai kaji an ce Kasagi na Halima. Don haka baya ga diramar Kasagi akwai wasu sunayen wasannin kwaikwayon da ya aiwatar kamar irin su Karambana da Magana jari ce da na ambata tun farko.

Su wane ne abokan wasansa na dirama?
Kasagi ya aiwatar da wasannin kwaikwayo da kusan dukkan wanda ya shahara a fagen wasan kwaikwayo a arewacin Nijeriya, kamar su Ƙasimu Yaro da sauran abokan diramarsa, kasancewar a gidan talabijin ne ake shiryawa tare da tsara wasannin kuma a can ake nuna su.

Wane bambanci ke tsakanin wasan kwaikwayo a zamanin su marigayi Umaru ɗanjuma Kasagi da kuma na wannan zamanin?
Akwai banbanci sosai saboda bazan manta ba a makon da ya gabata har kuka sai da marigayin ya yi a wurin taron da na gaya maka na baje kolin fasahohi wanda aka shirya a Kaduna, ba komai ya saka shi kuka ba sai yadda yake ganin an yi watsi da al’adar Hausawa wurin shirya fina-finan Hausa a wannan zamanin, ya kuma nuna takaicinsa dangane da yadda ake yawaita rawa da waqa a fina-finan Hausa inda ya bayyana cewar idan ma ya kama sai an yi waƙar to dole sai da dalili.

Bangon littafin Kulɓa na Ɓarna

Ya kuma nuna rashin jindaɗinsa saboda daina amfani da kayan kiɗan Hausawa irinsu Ganga, Garaya, Jauje da sauransu, inda aka koma amfani da kiɗan Fiyano a fina-finan wannan zamani, saboda haka akwai bambance bambance ƙwarai, ni kaina na tattauna da shi a wurin taron inda ya bayyana mani cewar ya tattauna da gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari akan yadda za a kawo sauyi ta fannin shirya fina-finan Hausa ta yadda za su yi daidai da al’adun Hausawa. Ya kuma gaya mani cewar a matsayin sa na shugaban hukumar adana kayan tarihi a Katsina zai tabbatar an tattara kayan tarihi da na al’adun Hausawa an kuma killlace su don raya al’adun Bahaushe, sai dai Allah bai cika masa wannan buri nasa ba, mako ɗaya bayan wannan tattaunawar ta mu Allah ya karɓi rayuwarsa.

Wacce gudummawa wasannin kwaikwayon shi da rubuce rubucen shi ya bayar ga al’ummar Hausawa?
Alhaji Umaru Ɗanjuma ya bada gudunmawa da dama ba a fannin wasan kwaikwayo ba kaɗai, har da raya al’adun Hausawa, saboda littattafan da ya wallafa baya ga nazartar su da ake yi a jami’o’i da makarantun gaba da sakandare, hukumar shirya jarabawa ta yammacin ƙasashen Afrika ta na amfani da su wajen koyar da ɗalibai da kuma shirya ma su jarabawa kamar dai yadda na yi bayani a baya. Saboda haka tarihin adabin Hausawa ba zai taɓa mantawa da gudummawar da Alhaji Umaru Ɗanjuma Kasagi ya bayar ba, haka nan al’ummar Hausawa ba za su tava mantawa da tarihinsa ba saboda gudummawar da ya bayar ta fannin rubuce rubucensa kaɗai ya isa adinga tunawa da shi.

Wacce shawara zaka bawa masu shirya fina-finai a wannan zamanin akan su yi koyi da irin fina-finan da marigayin ya shirya don raya al’adun Hausawa?
To zamani ne, duk abinda zamani ya zo da shi dole a karɓa, sai dai ma su shirya fina-finai a wannan zamanin ya kamata su san yadda magabata suka aiwatar da nasu fina-finan wanda hakan yasa har yanzu ake tunawa da su kuma tarihi zai ci gaba da tunawa da su. Yau idan da sun aiwaitar da wani abu na baɗala ko rashin kyautawa to da ba za a tuna da su ba, saboda haka masu shirya fina-finai a halin yanzu ya kamata su dinga shirya fina-finai masu amfani ga al’umma, waɗanda za su fito da al’adun Hausawa.

Daga ƙarshe Manhaja ta ji ta bakin ɗaya daga cikin ‘ya’yan marigayi Umaru Ɗanjuma
mai suna Abubakar Umaru Ɗanjuma, wanda ya bayyana cewar haƙiƙa sun yi babban rashi. Ya kuma bayyana cewar mahaifinsu ya bar matan aure biyu da ‘ya’ya goma 13 da kuma jikoki, ya ƙara da cewa mahaifinsu mutum ne da kowa ke jin daɗin mu’amala da shi kasancewar ya na da son wasa da dariya. Daga nan sai ya miƙa saƙon godiyarsa bisa ziyarar ta’aziyya da Manhaja ta kawo a gidansu dake a Sabuwar Unguwa cikin garin Katsina.