Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Amfani da man fetur na yau da kullum a Nijeriya ya ragu matuƙa bayan da Shugaba Bola Tinubu ya hau karagar mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Bayanan da gidan Talabijin na Channels ya samu daga Hukumar Haƙowa da Tace Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), ɓangaren adadin manyan motocin da ake fitarwa, ya nuna cewa yawan amfani da mai ya ragu ya zuwa ranar 20 ga Agusta, 2024, wanda ya kai lita miliyan 4.5 a kowace rana.
Yawan man fetur na yau da kullum kamar na Mayu 2023 ya kasance lita miliyan 60,000 a kowace rana, a cewar NMDPRA.
Kiyasin yana kawo raguwar amfani da fetur na yau da kullum da kashi 92 bayan 29 ga Mayu, 2023.
Binciken rahoton, abin mamaki, ya nuna cewa a cikin jihohi 36 na tarayyar Nijeriya, jihohi 16 ne kawai suka samu rabon kason kayayyakin da kamfanin man fetur na ƙasar NNPCL ya samu a cikin watan da ake yi.
Wannan yana nufin cewa waɗannan jihohin da ba su sami rabon kayayyakin ba sun sha wahala a cikin watan Agusta.
Binciken yadda NNNPCL ta raba kayayyakin a tsakanin jihohi 16, ya nuna cewa Neja ce tafi kowacce jiha rabon manyan motoci 21, wanda ya kai lita 940,000 a kullum, Legas ta samu na biyu a cikin manyan motoci 12 da ya kai lita 726, 001, Kaduna ta samu motoci 12 na lita 454,001.
Sauran jihohin kamar su Oyo sun samu tireloli 12 mai lita 454, Kano 9 tirela, Ondo 6, tirela 6, Edo 4, da manyan motoci FCT 4.
Irin su Sokoto sun karɓi manyan motoci 4 daga hukumar NNPCPL, jihar Ogun ta samu motoci uku, Osun uku, Gombe ɗaya, Benue ɗaya, Ekiti ɗaya da Kebbi.
A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne shugaba Tinubu ya ayyana kawo ƙarshen tallafin man fetur wanda a wancan lokacin ya salwantar da kusan Naira tiriliyan 12 cikin shekaru 10.
A cewar shugaban, biyan tallafin man fetur zai tsaya cak, domin ya jefa ƙasar cikin manyan basussuka.
Farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabo daga Naira 195 kan kowace lita zuwa kusan N1300, lamarin da ya sa hauhawar farashin man fetur ya kai kusan shekaru uku da ya kai kashi 34.19 cikin ɗari a watan Yuni. Tun daga lokacin ya ragu zuwa kashi 32.7 a cikin watan Satumba.
Haka kuma tsadar rayuwa ta yi tashin gwauron zabo, inda ya jefa ‘yan Nijeriya miliyan 129 cikin talauci, kamar yadda sabon rahoton Bankin Duniya ya nuna.