Adadin hada-hadar kuɗaɗen RMB tsakanin Sin da ƙasashen dake cikin shawarar BRI ya ƙaru a shekarar 2021

Daga CMG HAUSA

Adadin hada-hadar biyan kuɗin ƙasar Sin wato RMB tsakanin ƙasar Sin da ƙasashen dake cikin shawarar “ziri daya da hanya ɗaya” ko kuma BRI a taƙaice ya karu a shekarar 2021, inda adadin ya kai kuɗin Sin yuan tiriliyan 5.42, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 763.4, wanda hakan ya nuna ƙaruwar kaso 19.6 bisa dari cikin shekara guda, kamar dai yadda wani rahoto na babban bankin ƙasar ya bayyana.

Babban bankin na Sin, ya ce wannan hada-hada ta kai kaso 14.8 bisa dari, cikin jimillar hada-hadar da ƙasar Sin ta gudanar da kuɗin na RMB, tsakanin ta da ƙasashen ƙetare a shekarar ta bara.

Kazalika rahoton ya ce adadin kuɗaɗen da aka biya da RMB, a fannin cinikayyar hajoji, sun ƙaru da kaso 14.7 bisa ɗari, yayin da na jarin kai tsaye da aka zuwa ya kai kaso 43.4 bisa ɗari.

Rahoton ya ƙara da cewa, ya zuwa ƙarshen shekarar 2021, ƙasar Sin ta sanya hannu kan yarjejeniyar musayar kuɗaɗe da ƙasashe 22, masu nasaba da shawarar ziri daya da hanya daya, ta kuma kafa tsarin biyan kuɗaɗe da RMB tsakanin ta da ƙarin ƙasashe 8, dake cikin shawarar ta ziri ɗaya da hanya ɗaya.

Mai fassara: Saminu Alhassan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *