Adadin waɗanda suka rasu a harin masallaci a Kano ya ƙaru zuwa 15

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce adadin mutanen da suka mutu a harin da wani matashi ya kai wa wasu masallata a wani masallaci a Kano ya kai mutum 15,

Ana zargin cewa matashin ya watsa fetur a masallacin tare da cinna wuta, sannan kuma ya kulle ƙofar masallacin, tare da mutum kusan 40 a ciki.

Rahotonnin sun ce matashin ya kai harin ne sakamakon rigima kan rabon gado,

Shafi’u Abubakar ya yi zargin mutanen da ya cinna wa wutar mafi yawancinsu suna cikin Masallacin kuma sun cutar da shi a rabon gadon,

Tuni dai ‘yan sanda suka ce sun kama maharin mai shekara 38.

Lamarin da ya faru ranar Laraba lokacin da mutane ke gabatar da sallar asuba a garin Larabar Abasawa da ke cikin yankin ƙaramar hukumar Gezawa a jihar.

‘Yan sanda sun ce wanda ake zargin ya shaida musu cewa, ya aikata hakan ne da nufin ƙona wasu ‘yan uwansa da ke cikin masallacin waɗanda rigimar rabon gado ta shiga tsakaninsu.

“Abin da ya faru ba shi da alaƙa da ta’addanci, rigima ce da ta faru sakamakon rikicin rabon gado,” in ji Baturen ‘yan sandan yankin, Umar Sanda.