Adamu ya gargaɗi tsoffin gwamnonin APC su yi biyayya ga gwamnonin jihohinsu

Daga BASHIR ISAH

Yayin da zaɓen 2023 ke ƙara ƙaratowa, Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya gargaɗi ‘yan jam’iyyarsu da suka guji abin da ka iya haifar da rarraban kai a tsakaninsu.

Adamu ya yi wannan gargaɗi ne yayin taron shugabannin APC na ƙasa da ya gudana ranar Laraba a otel ɗin Transcop Hilton da ke Abuja.

Shugaban jam’iyyar ya tunatar da taron abin da ya faru da PDP a 2014 da kuma yadda PDPn ta faɗi zaɓe a 2015 saboda rashin haɗin kai a tsakanin ‘ya’yanta don ya zame musu izina.

Don haka Adamu ya ce, muddin APC na buƙatar ta ci gaba da samun nasara, ya zama wajibi ‘ya’yanta su kasance masu haɗin kai a kowane lokaci.

Haka nan, ya gargaɗi tsoffin gwamnonin APC kan cewa dole su zama masu biyayya ga gwamnonin jihohinsu saboda su ne shugabanni jam’iyya a jiha.

“APC na gargaɗin cewa gwamnoni masu ci su ne shugabannin jam’iyya a jihohinsu, don haka dole ne tsoffin gwamnoni su zamo masu biyayya a gare su,” in ji Adamu.

Ya ƙara da cewa yadda batun kuɗi ke shiga tsakanin gwamnoni masu ci da tsoffin gwamnoni a wasu jihohi, hakann ka iya haifar da farraƙa a jam’iyya.

Kaɗan daga cikin mahalarta taron sun haɗa da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo, gwamnonin APC, ciyamomin APC a jihohi da sauransu.