Adamu ya karɓi baƙuncin sabon zaɓaɓɓen Gwamnan Ekiti, Oyebanji

Daga BASHIR ISAH

A ranar Litinin Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya karɓi baƙuncin sabon zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Ekiti, Dr Abayomi Abiodun Oyebanji a gidansa da ke Abuja.

Oyebanji ya kai ziyarar ne bisa rakiyar Gwamnan Ekiti mai barin gado, Kayode Fayemi, domin gaisuwar ban-girma da ta ban-gajiya dangane da zaɓen gwamnan Ekiti da ya gudana a jihar a ranar Asabar da ta gabata wanda APC ta lashe.

Ko a Lahadin da ta gabata, Sanata Adamu ya aika wa zaɓaɓɓen gwamnan da wasiƙa ta musamman inda ya taya shi murnar nasarar da ya samu a zaɓen

Mr Oyebanji ya lashe zaɓen ne bayan da ya samu ƙuri’a 187,057, inda ya kayar da abokan hamayyarsa Segun Oni na SDP da Bisi Kolawole na PDP da sauransu.

Jam’iyyar SDP ce ta zo ta biyu a zaɓen da ƙuri’u 82,211, yayin da PDP ta zo ta uku da ƙuri’u 67,457.

Ya zuwa watan Oktoba mai zuwa ake sa ran za a rantsar da Mr Oyebanji a matsayin sabon gwamnan Ekiti don ya gaji mai barin gado Kayode Fayemi.