Adawa da siyasantar da matsalar tsaro ba za ta fisshe mu ba

A wannan yanayi da mu ke ciki yanzu na taɓarɓarewar tsaro a sassab Nijeriya, jam’iyyun adawa, ƙungiyoyi masu zaman kansu da ‘yan ba-ni-na-iya da kuma masu sharhi akan al’amuran yau da kullum a Nijeriya sun taso gwamnati gaba wajen sukar lamirin ta dangane da abinda ya shafi tsaron ƙasar.

Yayin da wasu suke kalaman tunzurawa da ɓatanci tare da nuna siyasa ƙarara a cikin kalaman waɗansu. Wanda hakan yake ƙara rura wutar ƙiyayya tsakanin talaka da masu mulkin, talakawa ba sa ganin ƙoƙarin da gwamnati ke yi, har ta kai ga wasu na tunanin yi mata bore.

Wasu kuwa suna yin suka ce mai ma’ana da nufin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki a lamarin tsaro da su farka don daƙile matsalolin ƙasar da suka ta’azzara. Kashe-kashe da sace-sacen mutane da dukiyoyin su ya zama ruwan dare a Nijeriya musamman yankin Arewa.

Wanda kuma matsalar tsaron ne ta sa talakawa suka juya wa gwamnatin PDP baya a zaɓen 2015. Kowa a wancan lokacin yana buƙatar canji ta kowane hali indai zai zama silar farfaɗo da zaman lafiyar da aka san Arewa da ita.

Saboda haka kowa ya tanadi katin jefa ƙuri’ar sa domin shi ne makamin riƙewar su na zaɓar gwamnatin da suke ganin za ta share musu hawaye idan Allah ya sa ta kai ga ci; musamman al’ummar Arewa da suka wasa wuƙar su a lokacin, suka yi fitar farin-ɗango don tuttuɗa wa gwamnatin APC ƙuri’a tun daga matakin ƙasa har jihohi, duk domin su samu sa’idar hare-haren da ‘yan’yan ƙungiyar Boko Haram ke kai musu a jihohin arewacin ƙasar nan musamman jihohin Borno, Yobe, da Adamawa, inda abun ya fi ƙamari tun wancan lokacin.

Da yawa sun zaɓi gwamnatin APC ne saboda kyautata mata zaton komai zai kau, zai zama tarihi, bayan wuya sai daɗi kamar yadda ɗan takarar yake bayyanawa a yayin yaƙin neman zaɓen sa, kuma wanda ya sanya a jadawalin alƙawuran sa na cewa zai tabbatar da tsaro cikin watanni uku kacal idan Allah ya ba shi nasara a zaɓen na 2015, bayan alƙawarin farfaɗo da tattalin arziki da kuma shata layi akan masu cin hanci da amsar rashawa a Nijeriya.

Sai ga shi a halin yanzu mutanen da suka bi gida-gida suna roƙon jama’a su zaɓi gwamnatin ta APC yanzu sun koma jin kunyar mutane, saboda ana musu shaguɓen cewa komai a ƙasar ya damalmale, abubuwa sun rincaɓe, kayan masarufi ya yi ɗan-karen tsada, tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a ya gagara, tattalin arzikin ƙasa ya durƙushe, talakawa suna ta ɗanɗana kuɗar su; ilimi ya gagari ‘ya’yan talakawa sakamakon ɗan-karen tsada da yake yi kullum. Da dai abubuwa birjik ga su nan da ake ganin gwamnati ta kasa taɓuka komai a kai.

Wanda hakan ya sa wuraren hirarrakin jama’a da majalisun zauniyar mutane da dandamalin sada zumunta dangin Facebook, Twitter da ma WhatsApp suke cika da saqonni iri-iri da suke nuna Allah-wadai da tofin Allah-tsine. 
Rubuce-rubuce, hotuna da ma faya-fayen bidiyo da na sauti sai karakaina suke yi ɗauke da kalaman tsinuwa, fushi da jafa’i wanda duka hakan na nuni kan cewa turar fa ta kai bango. Kuma ƙawancen da ke tsakanin talaka da gwamnatin APC musamman ma Shugaba Buhari kamar ta fara kaiwa ƙarshe.

An ci Talatar, Larabar ta watse, domin bayan maganganun ɓacin rai a wasu wuraren ma har an sha yin zanga-zangar nuna ƙin jinin gwamnati, wadda ko alama ba a yi mata zaton haka ba. A duk cikin waɗannan abubuwa da suke faruwa abinda mutane suka fi lura da shi shi ne nadama da takaicin yarda da amincewar da mutane talakawa, musamman na yankin Arewa, suka yi wa shugaban gwamnati mai ci, wato Muhammadu Buhari.

Talakawa sun sha ji da ganin faya-fayen bidiyo da na sauti masu yawa na irin maganganun da yake na alƙawarurruka ga jama’a da wasu faye-fayen da suke nuna irin bidiri da mutane suka yi lokacin da aka ayyana cewa shi ne ya lashe zaven shugabancin ƙasar nan a shekara ta 2015.

Amma ga shi yanzu talakawan da suka sha rana, yunwa da ƙishirwa akan layin zaɓe don ganin gwamnatin APC ta yi nasara, sai ga shi yanzu su ne suke zaman ɗar-ɗar a garuruwan su walau ƙauyuka ko birane. Domin yanzu babu wani wuri da mutum zai bi ya wuce salin-alin ba tare da fargabar masu garkuwa da mutane ko wasu ‘yan fashi ba; hatta na cikin gidaje ba su tsira ba. To yanzu ina talaka zai sa kan shi?

Sojojin Nijeriya da aka san su da ƙwarewa wajen kwantar da kowace iriyar tarzoma walau ta yaƙi ko fafatawa da masu tada ƙayar baya, a wasu qasashen Afrika, kamar su Laberiya da Saraliyon da sauran ƙashe, ciki kuwa har da na turawa an sha aike musu da gudummuwar sojojin Nijeriya, kuma suna kwantar da kowace iriyar matsala a ƙasar da aka tura su.

Yau an wayi gari shekaru kusan 12 ko fiye da haka ana fama da matsalar Boko Haram da masu garkuwa da mutane, satar dabbobi da rikice-rikicen Fulani makiyaya a jihohin Taraba da Benuwai da kuma wani yanki a jihar Filato. Sai rikicin addini da ƙabilanci a ƙudancin Nijeriya da ya ƙi ci ya kuma ƙi cinyewa. Har yanzu kuma gwamnati ta kasa fito da dabarun sanyaya wa talakawa rai ta hanyar magance wannan ta’addanci da kisan gillar da ake yi kullum ranar duniya.

A yanzu ɓarayin daji masu garkuwa da mutane, suna kai hare-hare a duk inda ran su ke so, cikin izza da nuna kamar gwamnati ba koman-komai ba ce a wajen su, su kashe na kashewa su sace na sacewa, sai an biya kuɗin fansa.

Inda za a gane sun gane wallen gwamnatin shi ne, yanzu sun fi mayar da hankali ga satar ɗalibai ‘yan makaranta, dalili kuwa shi ne sun tsaga sun ga jini, ma’ana tun da suka fara satar ɗaliban suka ga da riba, kuma gwamnati na musu abinda suke so ta hanyar ko dai a ba su kuɗin fansa ko kuma yarjejeniyar sakar masu ‘yan’uwan su da ke tsare a hannun jami’an tsaro, kamar yadda ta faru da ɗaliban Kagara a jihar Neja, da na Kwalejin Gandun Daji a jihar Kaduna da kuma wasu da yawa a jihar Zamfara.

Wannan ba ƙaramin abin kunya ba ne ga gwamnati mai cikakken iko wadda talakawa suka ɗora; ko babu komai ya kamata gwamnatin ta dinga yi wa talakawa maganganu masu daɗi na kwantar da hankali. Ba kowane shugaba ko wani jami’i a gwamnati ya dinga furta kalaman da ya ga dama ba, wanda za su iya hassala talakawa.
Amma duk da haka, ya kamata duk wani abu da ya shafi tsaro a dinga duban shi da muhimmanci da kuma idon basira, a daina siyasantar da shi, a haɗa ƙarfi da ƙarfi gabaɗaya, domin ita dai lafiya daɗi gare ta, babu kuma wanda zai ce bai son zaman lafiya da kwanciyar hankali. Kuma shi ɗan ta’adda ba ruwan sa da jam’iyya kaza kake, ko ɗan ƙungiya kaza, ko malam wane, a’a suna aiwatar da ta’addancin su akan kowa.

Saboda haka matsalar tsaro tana da muhimmanci, kowa yana da gudummuwar da zai bayar akai domin a samu zaman lafiya, idan kai talaka ne ka kula da makobcin ka ko baƙon da ya shigo unguwar ku wanda ba ka gane masa ba, ka sa ido sosai, ka kai rahoton duk wanda ba ka gane masa ba. Idan ka soma daga kan ka to za a samu canji matuƙar gaske, a maimakon a tsaya wannan na sukar wannan, wancan na zagin wancan, ko kuma ana adawa mara ma’ana akan yadda gwamnati ke yaƙi da ta’addanci ko yi mata zaton ƙasa.

Ita kuma gwamnati ta zama ba ta ji ba ta gani akan ‘yan adawa da nuna ƙiyayyar ga gwamnati matuƙar hanyar da ta ɗauka tana ganin za ta iya cimma nasara a yaƙin da take yi da ‘yan bindiga da sauran ƙungiyoyin ‘yan ta’adda. Saboda haka adawa da siyasantar da matsalar tsaro ba za ta fisshe mu ba, sai dai ma ta ƙara rura wutar matsalar.