Addini da siyasa: Tsakanin maguzanci da Musulunci a ƙasar Kano (3)

Daga FATUHU MUSTAPHA

Ci gaba daga makon jiya

A makon da ya wuce mun ji yadda Sarakunan Bagaudawa da haɗin kan malaman Musulunci suka haɗu suka yi wa Tsumburbura korar kare, mun kuma ji yadda har suka yi mata rakiya har sai da ta bar musu gari. To a wannan makon za mu ji kuma, shin mai ya biyo bayan wannan dambarwa da aka shafe ɗaruruwan shekaru ana fafatawa?

Kamar dai yadda muka faɗa a wancan makon, Musulunci ya yi nasara a kan maguzanci, to amma kuma wannan nasara da ya yi bai kuma sanya mutanen Kano sun amin ce sun karɓi Musulunci ba, su dai dama sarakunan Bagaudawa buƙatar maje hajji sallah, kuma sun samu buƙatar su ta biya, sun ga bayan manyan abokan gabar su, in ma da wani abu da zai sanya ba za su saki Musulunci ba, bai wuce irin romon da suke ganin za su ci gaba da sharɓa ba, musamman ta hanyar ƙulla alaƙar diflomasiyya da manyan ƙasashen Musulunci, musamman na yammacin Afirka da kuma waɗanda ke Arewacin Afrika.

To amma duk da haka, ba su damu su faɗaɗa addinin ya zamana sauran maguzawan da suke a matsayin talakawan su sun amince sun karɓe shi ba. Su dai sun ci gaba da addinin su da suka samu sabo ful, amma fa ba su ce dole sai maguzawa sun yi ba, abin da dai suke buƙata a wurin su shi ne su tabbatar sun musu ɗa’a, wacce a da suka ƙi suyi musu su ke yi wa abin bautar su.

Wani abin mamaki shi ne, yadda manyan Maguzawan da suka amince da su yi musu biyayya aka ƙyale su suka ci gaba da rayuwar su ba tare da wata kyara ba. Musamman in aka yi la’akari da Madaki Goje, wanda ya yi uwa ya yi makarɓiya a wannan gwagwarmaya, ya taimaka wurin ganin Bagaudawa sun yi nasara. Wannan rawa da ya taka ya sanya aka ba shi zaɓin ya faɗi duk sarautar da ya ke so ayi masa, ya kuwa zaɓi sarautar Madaki, aka kuma cire na kai aka naɗa shi.

Amma fa duk da haka bai taɓa salla ba, bai ma yarda da ita ba, har ma kirari ake masa ana “Goje kai wa Sallah girma, Goje maigida a bakin wuta….” Wannan ya nuna cewa, ba wai Musuluncin ne a gaban su ba, babban maƙasudin dai shi ne su samu su mallaki ƙasar Kano, kuma buqatar su ta biya.

Ta ɓangaren Malaman kuwa, su ma dai ko ba komai buƙata ta biya, domin dai koda talakawan ƙasar ba su amince sun karɓi addinin Musulunci ba, sun ci gaba da addinin su na iyaye da kakanni, amma duk da haka ai sarakunan ƙasar a yanzu dukkan su musulmi ne, kuma sun rungumi Musulunci saboda irin alfanun da suka tsinkaya zai haifar wa ƙasar ta su a nan gaba. Dan haka suka zaɓi su daure su ƙara haƙuri, wata rana mai haƙuri zai dafa dutse ya sha romon sa.

Su kuwa Maguzawa da aka ci da yaƙi, aka tabbatar musu da babu wani sarki sai Allah, sun amince da lallai an kai su ƙasa, to amma wannan bai sanya sun amince sun bar addinin su na gado ba. Shaidu na tarihi sun tabbatar da cewa, duk da cewa an kori gunkin na su da suke bauta wa, amma kuma ba su rabu da yi wa wurin ibadar ta su hidima ba. Har sai bayan da sarkin Kano Shashere ya kafa musu dokar ta ɓaci, ya umarce su da su tarwatse daga Dutsin Dala sannan suka bar wurin. Wannan shi ya tabbatar musu da cewa lallai wannan addini na su ya zo ƙarshe.

To amma fa bayan dara akwai wata cacar, Hausawa kan ce wai, kowa ma da ranar sa, mai ido ɗaya ya leƙa buta. Domin dai Bagaudawa sun yi nasara sun samu mulkin Kano, bayan shafe shekaru suna gwagwarmaya, to amma kuma har yanzu sun lura akwai sauran rina a kaba. Domin kamar yadda tarihi ya lura, suna da ƙasa ne, amma ba su da mutanen ƙasar. Wato suna mulkin ƙasar Kano, amma kuma ba su da wata ƙuwwa a kan mutanen ƙasar Kano.

Saboda haka zama marina ake tsakanin talakwan ƙasar da sarakunan ƙasar, kowa da inda ya kalla. Wannan ta sanya a karo da dama, ba su yi nasara akan abokan gaba a fagen yaƙi. Domin su dai Maguzawa waɗanda su suka fi yawa, ba za su amince su taimaka musu su shigar musu yaƙi ba, su kuma Sarakunan na ganin sun wuce su ɓata lokacin su su nemi gudunmawar su. A lokuta da dama  da suka yi yunƙurin su yaƙi Ƙasar Zazzau abin bai nasara ba, saboda rashin isassun  mayaƙa, duk kuwa da gashi suna da sabbin dabarun yaƙi da suka fi na Zazzau, to amma ba su da yawan sojin da za sun iya yaƙar ƙasar Zazzau ɗin.

Wannan ta sanya a lokacin da Kanajeji ya hau gadon mulki, sai ɗaya daga cikin tsoffin limaman Tsumburbura ya ba shi shawara ya ce masa “ba za ka taɓa nasara a kan Zazzau ba sai ka mallaki talakawan ƙasar nan, ba kuwa za ka mallake su ba har sai ka raya wannan abin da kakannin ka suka wargaza.” To kasan dan Adam da buri, musamman a lokacin baya da wani burin da ya wuce na yakaf tarihin shi ya fara cin Ƙasar Zazzau da yaƙi.

Dan haka ya ɗauri aniyar bai wa Tsumburbura dama a karo na biyu. Amma shi fa sarkin Kano duk wannan abu da ya ke faruwa ba addinin ne ya dame shi ba, abin da ya dame shi shi ne burin sa siyasa akan Ƙasar Zazzau ya tabbata, ya keta ruwan  tsafin nan na su na Kubanni da yake Shika, ya tarwatsa su daga kan Dutsen Kufena, musamman saboda ganin yadda suke qoqarin taimakwa Santolo su yi masa tawaye.

Da wannan buri a zuciya Kanajeji ya amince da a dawo da Tsumburbura, dan haka Samagi ya tattaro kayan tsafin sa da matsafan sa, ya kuma yi wasu al’adu, nan da nan kuwa sai ga shurin su da suke bauta ya bayyana. Wannan abu da kanajeji ya yi ya sanya ya samu kima da qwarjini a idon dubbun maguzawan da ke Ƙasar Kano. Sun amince da shi a matsayin sarakin su, duk kuwa da ba wata shiadar da ta tabbatar cewa ya tava yin bautar gumakan a zamanin mulkin sa hasali ma a wannan lokaci, ɗan sa kuma magajin sa, Sarkin Kano Umaru yana Borno yana karatun addini mai zurfi. Kuma anyi ittifaƙin a sarakunan Kano daga abinda ya bayyana ba a yi sarki mai taƙawar sa ba. To amma Hausawa kan ce “ran biyan buqata, rai ba komai bane in ji quda. Dan haka abinda yak enema ya samu.

Ba a yaƙi sai da uwa, koda kana da makamai da dabarun yaƙi irin na zamani, amma dole kana buƙatar isassun mayaƙan da za su yi maka yaƙin. Saboda haka shi Kanajeji babban burin sa shi ne ya samu Maguzawa su yadda su bi shi yaƙi ya ci ƙasar Zazzau da yaƙi. Wannan ne ya kai shi ga raya Maguzanci ba wani abu ba. Abin da kuwa yake nema ya samu. Dan haka bai tsaya wata wata ba, ya far shirin yaƙi zuwa Shika, inda ya ke fatan ya ci ƙasar da yaƙi. Ya kuwa samu nasarar samun haɗin kan dukkanin manyan Maguzawa, suka ba shi haɗin kai. A wannan shekarar ya kai wa Zazzau hari, ya ƙone Shika ya shiga cikin ruwan Kubanni ya yi yadda ya so. Dalilin tashin hedikwatar Zazzau daga nan kenan, ta koma Turunku.

Babban abin lura dai a nan shi ne, yadda tun usul shugabanni ke amfani da addini dan biyan bukatun su na siyasa. Yadda dama can shugabanni kan rainawa talaka hankali da sunan addini domin su tursasa masa ya yi musu biyayya. Mun ji yadda Bagauda ya zo Kano da buƙatun sa na tattalin arziki, wanda su kuma a wurin malaman addini Maguzawa ya saɓa da buƙatar su ta addini, dan haka dole kodai ya bari ko kuma sai inda ƙarfin su ya ƙare.

A ƙarshe mun ji yadda biyan buƙatar sa a Kano ta zamar masa nakiyar kan kashi, domin ga dai ƙarfen da yake nema don yin ƙira banza, ga kuma dabbobin da ya ke son ya yi farauta suma birjik, amma kuma ba damar taɓawa. A wurin su Bagaudawa wannan rashin adalci ne, amma a wurin su Maguzawa wannan keta alfarmar addinin su ce. Wanda kuma sai dai a ƙarar da irin su amma ba za su yadda a keta musu alfarma ba. A saboda haka suka tura shi gudun hijira Sheme can gaba da Kazaure. Tun daga nan aka ƙulla gadajjiyar gaba a tsakanin waɗannan ƙabilu guda biyu, ita ce gabar da sai da aka shafe sama da shekaru 600 ana gwabzawa.    

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*