Ado Doguwa ya lashe zaɓen Ɗan Majalisar Wakilai na mazaɓarsu

Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Alhassan Ado Doguwa, ya lashe zaɓen ɗan Majalisar Wakilai na Mazaɓar Tudun Wada/Doguwa a Jihar Kano.

Doguwa ya lashe zaɓen ne yayin zaɓen cike giɓi INEC ta gudanar a ranar Asabar.

Baturen zaɓen, Farfesa Sani Ibrahim, shi ne ya bayyana sakamakon zaɓen inda ya ce ɗan takarar Jam’iyyar APC, Ado Doguwa, ya lashe zaɓen ne da ƙuri’u 41, 573.

Ya ce ɗan takarar Jam’iyyar NNPP, Yushau Salisu ne ya zo na biyu da ƙuri’u 34,831, yayin da ɗan takarar Jam’iyyar PDP ya zo na uku da ƙuri’u 2,111.