Daga BASHIR ISAH
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), ya ba da sanarwar zai ƙara kuɗin wuta ya zuwa 1 ga watan Yulin 2023.
Cikin sanarwar da ya fitar ranar Lahadi da daddare, AEDC ya ce buƙatar ƙarin wutar ta taso ne duba da yadda darajar Naira ke hawa da sauka a kasuwar canji.
Sanarwar ta ce: “A sani, daga ranar 1 ga Yuli, 2023, za a yi ƙarin farashin wutar lantarki sakamakon hawa da saukar da farashi ke yi a kasuwar canji.
“Farashin canji a ƙarƙashin ƙa’idojin MYTO na 2022 da ya kasance N441/$1 a da, yanzu yana iya ƙaruwa zuwa N750/$1 wanda hakan zai shafi kuɗin wutar lantarkin da kuke amfani da ita.
“Kostomomin da ke tsarin ‘band B’ da ‘band C’ waɗanda ke samun wuta na awa 12 zuwa 16 a rana, sabon farashin da ake sa ran su riƙa biya shi ne N100 kan kowane kWh.
“Haka su ma kostomomin da ke tsarin ‘Band A’ (masu samun wuta na awa 20 zuwa fiye da haka) da kuma waɗanda ke tsarin ‘Band B’ (masu samun wuta na awa 16 zuwa 20), za su fuskanci ƙarin farashi.
“Kostomomin da ke amfani da mitar iya kuɗinka iya shagalinka kuwa, muna ba ku shawarar ko loda kati mai yawa kafin ƙarshen wannan watan saboda hakan zai ba ku damar cin gajiyar tsohon farashi kafin sabo ya fara aiki.
“Su ma masu biyan kuɗin wuta bayan sun amfana da ita, ku ma za ku ga ƙari daga watan Agusta,” in ji sanarwar.