Afirka ta Kudu ta fasa shirin yi wa ‘yan ƙasar rigakafin korona

Daga AISHA ASAS

Ƙasar Afirka ta Kudu ta ce ta fasa shirin yi wa ‘yan ƙasar allurar rigakafin cutar korona da ta so somawa bayan da ta gano cewa gwajin maganin AstraZeneca jab da ta yi ya kasa yaƙar nau’in cutar da ya bayyana a ƙasar.

Afirka ta Kudu ita ce ƙasar da ta fi kowace ƙasa harbuwa da cutar a faɗin nahiyar Afirka, inda ta so soma aiwatar da shirin yi wa ‘yan ƙasar allurar rigakafin korona da ta mallaka daga AstraZeneca da Oxford.

A cewar Ministan Lafiyar ƙasar Zweli Mkhize, “Mun dakatar da rigakafin na wucin-gadi har sai mun warware waɗannan matsaloli.”

Jami’ar Witwatersrand da ke Johannesburg ita ce ta gudanar da aikin gwajin maganin AstraZeneca inda ta ce bincikenta ya gano maganin ba shi da ƙarfin yaƙar cutar korona mara tsanani a ƙasar balle kuma mai tsananin.

Sai dai a nasa ɓangaren kamfanin AstraZeneca ya ce mutum 2000 da aka yi amfani da su wajen gwajin babu ko guda da ya nuna wata alama mai tsanani wanda a cewarsa kenan za a iya amfani da maganin wajen magance wasu cututtukan na daban duk da dai ba a kai ga tabbatar da hakan ba a yanzu.