Ahir ɗinku da tsoma hannu a zaɓen 2023 – Janar Yahaya ga sojoji

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Nijeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya, ya ja kunnen manya da ƙananan hafsoshin sojan ƙasa na Nijeriya da su cigaba da kasancewa ba tare da nuna ɓangaranci ba wajen gudanar da ayyukansu a lokaci da kuma bayan zaɓen 2023.

Janar Yahaya ya bayar da wannan umarni ne a taron ƙara wa juna na yini biyu kan Tsarin Aiki da Gudanarwa na hafsoshin sojojin Nijeriya, wanda sakataren ma’aikatar soji ta shirya a ranar Talata a Abuja.

Babban Hafsan, wanda ya samu wakilcin shugaban Kawo Canje-canje da Ƙirƙire-ƙirƙire, Maanji Janar Charles Ofoche, ya ce, dole ne jami’an soji su kasance masu ƙwarewa kuma su aiwatar da duk aikin da aka ba su.

Ya ƙara da cewa, taron ƙarawa juna sani na daga cikin ƙoƙarin da rundunar sojojin Nijeriya ke yi na ganin jami’anta sun ci gaba da saun ƙwarewa wajen gudanar da ayyukansu a faɗin ƙasar.

“Ina so in yi amfani da wannan dandali domin nanata buƙatar kowa ya ci gaba da kasancewa ba tare da nuna ɓangaranci ba yayin da muke tunkarar babban zaven 2023.

“Ana qoqarin ganin kowanne jami’ai kafin zaɓe da lokacin zave da kuma bayan zaɓe ya ci gaba da kasancewa cikin ƙwarewa da kuma fifikon shugabanci. Saboda haka, ina roƙon ku duka da ku nuna mafi kyawun ɗabi’a yayin gudanar da zaɓe,” inji shi.

Hukumar ta shugaban ta ce, shigar da jami’an sojin Nijeriya a wasu ayyuka da dama a faɗin ƙasar ya haifar da buƙatar samar da ingantaccen tsarin aiki don samar da shugabanci nagari a tsakanin jami’an.

A cewarsa, ya zama wajibi a inganta tsarinmu na tsare-tsare na sana’o’i, da kuma kula da ma’aikata domin tabbatar da daidaito da kuma walwala ga jami’ai.

Ya ce, taron ƙarawa juna sani zai ba wa mahalarta damar fahimtar sabbin manufofin diflomasiyya, nazarin sojojin Nijeriya da rawar da jami’ai ke takawa wajen cimma manufofi a ƙasar.

“A matsayinmu na jami’an soja, ya kamata mu tuna da buƙatar yin shiri sosai don yin aiki a cikin mahallin haɗin gwiwa da tura su zuwa inda za su iya samar da sabbin tsare-tsare, matakai, da dabaru don saduwa da sauyin yanayin fagen fama.

“Saboda haka, ya zama wajibi mu ci gaba da zage-zage tare da zaburar da jami’anmu da mazajenmu ta hanyar ingantaccen tsarin tsara ayyuka,” inji shi.

Sakataren sojin, Manjo Janar Jamal Abdulsalam, ya ce, taron ƙara wa juna sani yana da nasaba da cewa sarrafa ma’aikata na bayar da gudunmowa ba kaɗan ba wajen bunƙasa ƙwararrun ma’aikata domin samun kyakkyawan aiki a ayyukan haɗin gwiwa da kuma bai ɗaya.

Abdulsalam ya ce, an shirya taron ne domin sauƙaƙa fahimtar ƙa’idojin da ake buƙata domin sanya hafsoshin sojojin Nijeriya.

A cewarsa, hakan ne don ba su damar cimma kyawawan ayyuka a duniya da kuma buƙatar gudanar da aikin da ya dace na tsara ayyukan hafsoshin soja.

Ya ce, Shugaban Hafsan Sojin ƙasar ya ba da fifiko kan horar da jami’an da horar da su daidai da falsafar umarninsa da suka haɗa da ƙwarewa, shiri da gudanar da aiki yadda ya kamata a Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *