Aikin shimfiɗa bututun gas ya cimma kashi 73 da kammaluwa – Darakta Ahmed

Daga BASHIR ISAH

An bayyana cewa kawo yanzu, aikin shimfiɗa bututun gas da gwamnatin Buhari ke yi daga Ajaokuta zuwa Kaduna zuwa Kano ya kai kashi 73.3 cikin 100 da kammaluwa.

Darakta a sahen makamashin gas na Kamfanin Fetur na Ƙasa, Injiniya Abdulkadir Ahmed ne ya bayyana hakan a wajen wani taro da ya gudana ran 5 ga Maris.

Ahmed ya ƙara da cewa, jihar Kaduna za ta ci moriyar wutar lantarki mai ƙarfin megawat 900 idan an kammala aikin.

Idan dai za a iya tunawa, gwamnatin Buhari ta soma aiwatar da aikin shimfiɗa bututun gas ɗin ne tun a watan Yulin 2020 da zummar fito da damarmakin aiki da harkokin kasuwancin da sashen gas ke tattare da su, haɗe da samar da gas ɗin a farashi mai rahusa don amfanin ‘yan ƙasa.