Aikinku na iya kai ku wuta ko aljanna – Dambo ga ‘yan jarida

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Sarkin Fawa Dambo ya gargaɗi ‘yan jarida da ke aiki a jihar da su yi adalci a cikin rahotannin su, inda ya ce aikin na iya kai mutum wuta ko aljanna a ranar gobe ƙiyama.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karɓar mambobin ƙungiyar ‘Correspondents Chapel’ da ke tare da sabon zaɓaɓɓen sakataren ƙungiyar shiyya ta ‘A’ ta ƙungiyar ‘yan jaridu ta ƙasa wato NUJ, Abdulrazak Bello Ƙaura wanda ya kai masa ziyarar taya murna ranar Laraba.

Alhaji Abubakar ya kuma ƙara da cewa, babu wani ci gaba mai ma’ana da za a iya samu a tsakanin ‘yan jarida idan suna yaɗa labaran ƙarairayi.

“Ina so in yi amfani da wannan kafar domin jawo hankalinku ku lura cewa, aikinku a kowace al’umma shi ne mafifici kuma abin da kuka rubuta mai kyau ko mara kyau zai iya kai ku wuta ko aljanna, kamar yadda dukkan mu za mu yi lissafin ayyukanmu a gaban Allah Maɗaukakin Sarki a ranar lahira,” ya ce.

Ya kuma yi kira ga ‘yan jarida da ke aiki a jihar da su guji duk wani rahoto da ya wuce gona da iri da ka iya haifar da damuwa, son zuciya ko vata sunan kowa saboda siyasa.

Ya ce ma’aikatar sa za ta ci gaba da jajircewa wajen yin aiki kafaɗa da kafaɗa da ‘yan jarida masu aiki a inda ya dace domin ci gaban jihar.

Da ya ke mayar da martani, sabon zaɓaɓɓen Sakatare na ƙungiyar ta NUJ ta Ƙasa, Kwamared Abdulrazak Bello Ƙaura ya ce sun ziyarci ofishin kwamishinan ne domin taya shi murna bisa naɗin da aka yi masa tare da neman goyon bayan ma’aikatarsa ​​domin cimma manufofin da ake buƙata.