Ainihin ma’anar farfaɗo da ƙasar Sin a sabon zamani

Daga CMG HAUSA

Ga duk mai bibiyar yadda babban taron wakilan JKS na 20 ke gudana, ba zai gaza jin jimlar “farfaɗo da ƙasar Sin daga dukkanin fannoni a sabon zamani da ake ciki” ba, musamman cikin rahoton da shugaban ƙasar, kuma babban sakataren kwamitin ƙolin JKS Xi Jinping ya gabatar, wanda hakan buri ne na raya ƙasar da JKS ta sha alwashin cimmawa.

A ƙarƙashin wannan manufa, akwai muhimman matakai masu dacewa da salon gurguzu mai sigar musamman da ƙasar Sin ke bi, wanda ya tanadi samarwa al’ummar Sinawa yanayin rayuwa mai cike da zaman lafiya da wadata, da zamanantar da tattalin arziki da zamantakewa, da bunƙasa al’adu, da kyautata alaƙar rayuwa tsakanin bil adama da sauran halittu, waɗanda sakamakon su zai amfani dukkanin sassan alummun ƙasar ba wai wasu mutane kalilan ba.

Idan muka kalli wannan salon samar da ci gaba na ƙasar Sin, za mu ga ya sha banban da na ƙasashen yamma masu bin salon jari-hujja, waɗanda tarihi ya jima da sanin su, a matsayin masu amfani da ƙarfin tuwo, da mulkin mallaka wajen faɗaɗa tasirinsu a duniya, da cimma muradun ƙashin kai ta kowace irin hanya.

Ko shakka babu, salon gurguzu mai halayyar musamman na Sin, ya haifar da babbar dama ta yakar talauci, inda ƙarƙashinsa ƙasar ta cimma nasarar tsamo al’ummarta da yawansu ya kusa miliyan 100 daga ƙangin talauci cikin shekaru 10 kacal, matakin da masu fashin baki ke ganin ya shiga tarihin duniya, a matsayin irin wanda ba a taɓa gani ba a shekarun baya bayan nan.

Alal haƙiƙa, JKS ta dora muhimmancin gaske ga moriyar al’ummar Sinawa. Jam’iyya ce da har kullum ke aiki tukuru, wajen ganin ba a bar wani rukuni na al’umma a baya ba a dukkanin fannonin ci gaba.

Ana kuma iya ganin hakan a zahiri, idan aka yi duba ga ɓangarorin da ƙasar Sin ta cimma manyan nasarori a cikinsu, kamar bunƙasar tattalin arziki, da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da faɗaɗar fannin ilimin kimiyya da fasaha, da ƙaruwar guraben ayyukan yi, da tsara manufofin inganta rayuwar tsofaffi da yara ƙanana da sauran su. Tabbas wannan kaɗan ne daga ainihin ma’anar matakan farfaɗo da ƙasar Sin a sabon zamani.

Mai fassara: Saminu Alhasan