Aisha Buhari ta buƙaci a kawo ƙarshen matsalar garkuwa da mutane

Daga BASHIR ISAH

Matar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, ta yi kira ga masu faɗa a ji na Nijeriya da su ci gaba da yin amfani da damarmakin da suke da su wajen kawo ƙarshen harkokin yin garkuwa da mutane tare da tabbatar da cewa yara mata na da kariya a duk inda suka tsinci kansu.

Aisha ta bayyana haka ne a saƙon taya murna ga ‘yan’uwata mata kan Ranar Mata ta Duniya, da ta wallafa a shafinta na twita.

Ta ce bikin ranar mata ta duniya, lokaci ne da kan bada damar a san irin nasarorin da aka samu wajen kula da sha’anin mata mayansu da ƙanana. Tana mai cewa, abin a yaba wa kokarin mata ne duba da irin rawar da suke takawa a fagen yaƙi da cutar korona.

Ta ci gaba da cewa cutar korona ta yi matuƙar tasiri a rayuwar mata, ta daburta musu sha’anin karatunsu, ta sa sun rasa aiki, ta jefa wasu cikin ƙangin talauci da sauransu.

Da wannan ta ce yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin yaƙi da annobar, haka ma akwai buƙatat a duba a bai wa waɗanda suka cutu da cutar don gyara musu rayuwa.