
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar Lauyoyi Mata ta Ƙasa (NBAWF), ta yi kira ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da su amince da gudanar da buɗaɗɗen bincike na adalci game da zargin cin zarafi da ya ƙunshi mutanen biyu.
Shugabar NBAWF, Barista Huwaila Muhammad Ibrahim ta yi kiran a yayin ganawa da manema labarai a ranar Asabar, ta na mai cewa babu wanda zai zama alƙali a ƙararsa.
Ta ce, yin hakan adalci ne ga sanatocin biyu, wanda zai bai wa Akpabio damar wanke kansa, da kuma bai wa Natasha damar tabbatar da zargin nata.
Ta kuma ce a matsayinsu na cibiyar lauyoyi mata a Nijeriya, sun amince da cewa, lallai ne kowane ɗan Nijeriya ya na da ƴancin kare mutuncinsa, girmama shi da kuma hana a ci mutuncinsa, kamar yadda dokar ƙasa ta tanadar.
NBAWF ta ƙara da cewa, rashin yin bincike game da zargin, zai buɗe ƙofar yin sako-sako ga wasu batutuwa da ka iya tasowa nan gaba.
Lallai yin adalci akan batun zai taimaka wajen cigaba da kare martabar majalisar a matsayinta na ɗaya daga cikin rassan gwamnati, kamar yadda ƙungiyar ta bayyana.