Akpabio ya bayyana ƙarin sunayen ministoci 19 da Tinubu ya aika wa Majalisar Tarayya

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana sunayen ministoci kashi na biyu da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya aika wa Majalisar domin tantacewa.

A ranar Labara Shugaba Tinubu ya tura wa Majalisar ta Dattawa da ƙarin sunaye 19 ta hannun Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila.

Sunayen da Tinubun ta tura wa Majalisar sun haɗa da tsaffin gwamnoni Bello Matawalle (Zamfara), Atiku Bagudu (Kebbi), Simon Lalong (Plateau), Ibrahim Geidam (Yobe) da kuma Isiaka Oyetola (Osun).

Sauran su ne, Abdullahi Gwarzo, Bosun Tijani, Maryam Shetty, Isiak Salako, Tunji Alausa, Yusuf Sunusi, Ibrahim Geidam, Lola John, Shuaibu Audu, Tahir Mamman, Aliyu Abdullahi, Alkali Saidu, Heineken Lokpobori, Maigari Ahmadu sai kuma Zaphaniah Jisalo.

Idan ba a manta ba, a makon jiya Tinubu ya aika wa Majalisar sunaye 28 domin a tantance su a matsayin ministoci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *