Daga BASHIR ISAH
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da kafa wasu kwamitoci a majalisar don gudanar da harkokin gwamnati.
Kwamitocin sun haɗa da na Kwamitin Kasafi, Kwamitin Kula da Asusun Gwamnati da Kwamitin Ɗa’a da Ƙorafe-ƙorafe.
Da yake jawabi yayin zaman majalisar a ranar Talata, Akpabio ya bayyana Sanata Solomon Adeola a matsayin Shugaban Kwamitin Kasafi, yayin da Sanata Ahmed Wadada zai jagoranci Kwamitin Kula da Asusun Gwamnati.
A hannu guda, Shugaban Majalisar ya karanto wa zauren wasiƙar da Shugaba Bola Tinubu ya tura wa majalisar ta neman tabbatar da shugabannin tsaron da ya naɗa kwannan nan.
Apkabio ya ce majalisar za ta yi aikin tantance shugabannin tsaron ya zuwa ranar da bai ambata ba.