Akwai ƙalubale ga marubutan da suka dogara da rubutu kawai – Safna Jawabi

“Sanadin ababen da ke ƙunshe a zuciyata na fara rubutu”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Mata marubuta sun daɗe suna ba da gagarumar gudunmawa a vangaren cigaban adabi da harkokin rayuwa, saboda burin su na ganin sun kawo gyara a cikin al’umma da irin damar da suke da ita. Safna Aliyu Jawabi wata fitacciyar marubuciyar yanar gizo ce, daga Jihar Neja, wacce ta yi suna wajen fitar da littattafai da ke cike da darussa masu muhimmanci. A zantawarta da wakilin Manhaja a Jos, Safna ta shaida masa cewa, burinta na amfani da muryarta wajen kawo sauyi a rayuwar al’umma shi ya sa ta mayar da hankali ga rubutu.

MANHAJA: Mu fara da jin cikakken sunanki da abin da ki ke yi a rayuwa.

SAFNA: Cikakken sunana shi ne Safnah Aliyu jawabi. Ni mutuniyar Jihar Neja ce daga ƙaramar Hukumar Suleja.

Ba mu taƙaitaccen tarihin rayuwarki.
Kamar yadda na faɗa ni ‘yar asalin Jihar Neja ce, kuma haifaffiyar garin Suleja. Na yi karatu daga matakin firamare har zuwa Kwalejin Ilimi da ke Abuja, wato College of Education Zuba. Ni ce autar mata a ɗakin mu, hakan ya sa zan iya cewa na taso cikin gata a gun iyayena. Ni marubuciya ce, kuma mai sana’ar ado da kwalliya ta mata, wato ‘make up artist’. Sannan Ina yin sana’ar yin kayan ƙwalama da soye soye, irin su alawar madara, gullisuwa da cake.

Wanne abu ne za mu iya cewa Safnah ta fi shahara a kansa tsakanin rubutu da sana’a?

Duka biyun gaskiya, amma dai a yanzu nafi mayar da hankali a kan sana’a ta.

Mai ya ja hankalinki ki ka fara sha’awar rubutun Hausa?

Na kasance ma’abociyar karance-karance, bayan haka akwai abubuwa da yawa da suke ƙunshe cikin raina musamman abubuwan da ke addabar ƙasata. Na yi tunani na ga ba ni da muryar da zan ɗaga a saurare ni, hakan ya sa na zaɓi yin rubutu don na isar da saƙo ga al’ummar ƙasata.

Kawo yanzu kin rubuta littattafai nawa?

Na yi littattafai da ɗan dama, da yawan su ya kai goma sha biyu. Su ne, ‘Ƙarshen Wahala’, ‘Yayana Ne Ko Mijina’? ‘Ni’imar Allah’, ‘Duk A Sanadin Soyayya’, ‘Butulci Ko Fansa?’ ‘Ismat’, ‘Amjad’, ‘Musaddam Ne Zavina’, ‘Duk Bugun Numfashi’, ‘Karfin Igiyar So’, ‘Ƴa Ko jika? ‘Baƙar Ashana’, sai kuma ‘Zaman Aure’.

Kin tava buga littafinki ne ko ke ma marubuciyar ‘online’ ce kawai?

Gaskiya ban tava bugawa ba, amma dai Ina da niyya, don yanzu haka ma akwai wani littafina da yake gab da shiga kasuwa, da yardar Allah.

Kina daga cikin haɗakar wasu marubuta goma da suke aikin rubuta wani littafi mai suna ‘Da Jininsa A Jikina’ mai ya baki ƙwarin gwiwar shiga cikin wannan haɗaka?

Eh, tabbas Ina cikin su. Kuma gaskiya abin da ya bani ƙarfin gwiwar shiga cikin wannan haɗaka dai na farko ita ce, ganin irin fasihan marubutan da aka haɗa a ciki. Na fahimci cewa lallai wannan aiki na jajirtattun marubuta zai zo da zallar basira da fasaha, saboda kowannen su gwani ne a ɓangaren sa. Kai tsaye zan iya cewa ni ce ƙarama kuma ɗaliba a cikin waɗannan zaratan marubuta.

A ina ki ke samun hikimar rubutun da ki ke yi?

Ta hanyar faɗaɗa bincike da bibiyar abubuwan da ke faruwa a ƙasata.

Bayan rubutun adabi kina da sana’a ta ado da kwalliya da ki ke yi. Me ya ja hankalinki ga wannan harka?

Gaskiya tun tasowata na tashi da sha’awar kwalliya, haka nan Ina zaune zan ɗauki ja gira na yi ta zanawa ‘yar tsanata kwalliya, da haka dai na girma da son kwalliya, daga baya kuma na shiga shagon koyo don na ƙware musamman irin wannan kwalliyar da ake yi ta zamani, Bayan na kammala kuma mahaifina ya buɗe min shagon kwalliya na kaina da na sa wa suna JAWABI’S TOUCH a nan kusa da Babban Asibitin Suleja. Ina aikina da masu taimaka min da sauran yaran aiki da suke koyon kwalliyar su ma, inda muke yin abubuwa masu yawa irin kwalliyar amare, dilka, wato wankan amarya, kuma muna yin lalle na gargajiya da na zamani.

Yaya za ki kwatanta nasarar da ki ke samu a rayuwarki daga waɗannan harkoki da ki ke yi?

To, Alhamdulla. Don kuwa na samu nasarori da dama a harkar rubutu da ma kuma sana’ar da nake ta bayan fage. A shekarar 2021 an karrama ni da shaidar girmamawa a Kano wajen taron Bakandamiya da aka gudanar. Sannan a shekarar 2022 an sake karrama ni da wata kyauta ta musamman a taron naɗin sarautar Alan Waƙa ta Sarkin Ɗiyan Gobir a nan birnin Kano. Bayan haka na shiga gasanni wanda ake yi cikin wani zaure a manhajar WhatsApp mai suna Marubuta inda a watan farko da aka sanya gasar ni ce ta farko da na yi nasara a wannan gasar.

Na kuma shiga gasar Ɗan Giwa wanda labarina ya zo ɗaya daga cikin 30 ɗin da aka ware. Na shiga gasar Gusau Institute inda nan ma dai labarina yana ɗaya daga cikin guda goma sha bakwai da aka zaɓa, hakan kuma ya sa suka karrama ni da shaidar karramawa.

Wanne ƙalubale ki ke da shi ga sauran matasan marubuta game da kama sana’o’in dogaro da kai?

A gaskiya dai akwai ƙalubale sosai ga matasan marubuta waɗanda suka dogara ga rubutu kawai babu aikin hannu, don kuwa aka ce da na gaba ake gane zurfin ruwa. Idan haka ne kuwa ya dace matasan marubuta mu nemi sana’a musamman idan muka dubi rayuwar jagoran mu Ado Ahmad Gidan Dabino, za mu ga bayan rubutu yana da sana’ar ɗab’in na buga littattafai, don har ofis yake da shi mai zaman kansa. Bayan haka ga Hajiya Fauziyya D. Sulaiman tana da aikin da take yi a Arewa 24.

Shin kina ganin rubutu a matsayin sana’a ne ko kina yi ne don sha’awa kawai?

Ina ɗaukar rubutu a matsayin sana’a, har wa yau kuma abu ne da nake yi saboda sha’awa. A dalilin rubutu na samu alheri sosai, kuma Ina alfahari da haka. Rubutu sana’a ce mai ƙarfi da mutunci a qasashen da suka cigaba, amma mu a nan Afirka muna buƙatar mu jingina da wata sana’a da za ta riƙe mu, don kula da rayuwarmu. Don haka yake da muhimmanci mu samu wata sana’a da zamu riqe kanmu da ita. Kamar yadda ni ma yanzu nake jin daɗin sana’ar da nake yi.

Yaya alaƙar ki take da masu bibiyar rubuce rubucen ki, ta yaya ki ke fahimtar yadda suke jin daɗin littattafanki?

Muna da alaƙa mai girman gaske ta yadda idan suka kwana biyu ba su ji motsina ba koda kuwa a waya ne ba su ganni ba sai an samu wanda ya kira ni daga cikin su yake tambaya ta ko lafiya. Sannan ta hanyar sharhi da suke aiko min da shi, da kuma yanayin da suke kirana tun da sanyin safiya, don na tura musu da cigaban labarin da nake yi a lokacin.

Wanne abu ne ya tava faruwa da ke a matsayinki ta marubuciya da ya faranta miki rai ko akasin haka, wanda ba za ki manta ba?

Gaskiya akwai abubuwa da yawa, amma ga kaɗan daga ciki. Abin da ya fi faranta min raina a duniyar marubuta ba komai ba ne face yadda marubutanmu musamman manya wanda duniya ta san da zaman su suka ɗauki al’amarina da girma, Na taɓa haɗa wata gasa a shekarar 2022, abin zai baka mamaki idan na ce maka kusan duk manyan marubutan mu waɗanda ake ji da su sun halacci wannan wurin musamman irin su Ado Ahmad Gidan Dabino, Alan Waƙa, Farfesa Yusuf Adamu, Hajiya Balaraba Ramat Yakubu da Hajiya Fauziyya D. Sulaiman da sauran su, duk sun je taron. Wannan abin ya faranta raina matuƙa, don kuwa na san idan ba don silar rubutu ba, ƙila ma har na bar duniya ba za mu tava haɗuwa ba.

Wanne darasi ki ka koya daga alaƙar ki da sauran marubuta?

Na koyi abubuwa da dama gaskiya, wanda kuma hakan ya taimaka min wajen samun kyakkyawar mu’amala da su.

Wacce ƙungiyar marubuta ki ke, kuma wanne tasiri ta yi a game da cigaban rubutunki?

Ina da ƙungiyar da nake wakilta a matsayin shugaba, wato Ƙungiyar Perfect Writers Association. Muna sanya gasa a tsakanin mambobinmu, lokaci zuwa lokaci. Bayan haka kuma muna bibiyar rubutunsu dan ganin mun ɗora su kan hanyar da ta dace.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarki?

Idan rana ta fito tafin hannu ba ya kare ta!

Na gode ƙwarai da gaske.

Masha Allah. Ni ce da godiya.