Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar Masu Sarin Fetur ta Nijeriya (PETROAN) ta bayyana cewa, farashin man da tsohuwar Matatar Fatakwal ta da dawo da aiki a ranar Talata ta saka, ya zarce Naira 75 a kowace lita fiye da wanda matatar Dangote ke sayarwa.
Jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar, Dokta Joseph Obele ne ya bayyana hakan a yayin bikin buɗe matatar man Fatakwal a hukumance, wanda yanzu haka yake aiki da gangar mai 60,000 a kowace rana.
Dr Obele, tsohon shugaban ƙungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Nijeriya IPMAN, ya yaba wa gwamnatin tarayya kan farfaɗo da tsohuwar matatar man, ya bayyana damuwarsa kan rashin daidaiton farashin man fetur da Kamfanin Mai na Nijeriya, (NNPCL) ke yi tsakanin matatar Fatakwal da matatar Dangote.
A cewarsa, yayin da matatar man Dangote ke sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kan Naira 970, farashin NNPC ya kai N1,045, sabanin Naira 75 kan kowace lita.
Ya ce, bambamcin farashin N75 wani babban rata ne ga ’yan kasuwa, musamman ga masana’antar da ribarta ta ta’allaƙa kan farashi.
Sai dai ya bayyana maido da matatar a matsayin wani gagarumin mataki na rage dogaron da Nijeriya ke yi kan man fetur da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.
Obele ya bayyana cewa babban jami’in NNPC, Mele Kyari, ya yi alƙawarin magance matsalar tare da daidaita farashin domin rage tasirin da yake yi wa ’yan kasuwa da sauran masu saye.
A ranar Talata, 27 ga watan Nuwamba, Hukumar NNPC ta sanar da cewa tsohuwar matatar mai ta Fatakwal ta fara aiki da kashi 70% kuma tana samar da ɗimbin albarkatun man fetur a kullum.
Wannan ya nuna wani ci gaba a cikin farfaɗowar matatar bayan shekaru da aka samu koma bayan aiki.