Akwai alaƙa mai ƙarfi tsakani na da Will Smith kafin marin Oscar, cewar ƙanin Chris

Daga AISHA ASAS

Biyo bayan bidiyon ban haƙuri ga Chris da jarumi Will Smith ya fitar wanda ya ambaci sunan ƙanin Chris Tony Rock a ciki, hakan ya ba wa ƙanin na Chris damar mayar da martani ga waɗanda suka yi ma shi ca a lokacin da ya tofa albarkacin bakinsu kan lamarin na marin da aka yi wa yayansa jarumi Chris.

Da yawa sun kira maganganun da Tony ya yi a matsayin katsalandan kan abinda bai shafe shi ba, sai dai kiran sunanshi da Will Smith ya yi ya ba shi damar sanar da masu ganin shishiginsa abinda ba su sani ba kan alaƙarsa da wanda ya shararawa yayansa mari a bainar jama’a wato Will Smith. Inda ya ce, “ban kasance daga waje ba ko ɗan amshin shata da ke neman suna a cikin rikicin Will da Chris ba. Akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanina da Will Smith.”

Will Smith ya fitar da biyon ban haƙuri ga jarumi Chris Rock, watanni huɗu bayan tsinke shi da mari a daidai lokacin da duniya ke tare da su a babban taron Oscar, dalilin yin barkwanci da sunan matarsa. Jarumin ya bayyana nadamarsa ga wannan ɗanyen aiki da ya aikata.

Will ya fara da neman gafarar mahaifiyar Chris wadda a baya ta bayyana rashin jin daɗinta kan abinda aka yi wa ɗanta har ta ƙara da cewa “lokacin da Will Smith ya mari Chris, ya mari dukkanmu ne. Tabbas har ni ya mara, domin duk wanda ya taɓa ɗana, tamkar ni ya taɓa.”

Shi kuwa Will Smith ya mayar mata da martani da cewa, “wannan shine tunanin da bai zo wa ƙwaƙwalwata ba, ban yi tunanin adadin mutanen da zan ɓata wa ba idan na aikata abin da na yi ba.

Don haka Ina neman gafarar mahaifiyar Chris, Ina mai ba wa iyalansa dukka haƙuri, musamman ma Tony Rock, wanda ya kasance amini gare ni. Tony Rock mutumina ne na ƙwarai, sai dai na sani wannan al’amari ya ruguza amintarmu.”

Waɗannan kalamai ne suka ba wa Tony Rock damar mayar da martani ga masu gwale shi yayin da ya tsoma bakinshi kan lamarin. “Ga waɗanda ke hargowa da faɗar maganganun banza a kafafen sada zumunta kan in kama bakina, in daina shiga sha’anin da ba a yi da ni ba, har suke jifa ta da kalmar neman a sanni ne na ke yi.

Yanzu kuma da aka ji wanda abin ya shafa ya kira sunana ne aka yi ta kaina, duk da cewa kaɗan ne a cikin kafafen sada zumunta masu hankalin fahimtar akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanina da Will Smith kafin abinda ya faru a ranar Oscar.”

Kwanaki kaɗan bayan faruwar marin, Tony Rock ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, bai gamsu da bayar da haƙuri ta rubutu da jarumi Will Smith ya yi ba, wanda wannan furucin na sa ne ya sa aka jefe shi da kalamai marar daɗi ba tare da tambayar dalilin sa ba.