Akwai buƙatar magance matsalar ɓatagarin ’yan jarida – NUJ

Daga RAMADAN SADA

Ƙungiyar ‘yan jaridu ta ƙasa (NUJ), reshen Zariya da ke jihar Kaduna, ta yi kira ga hukumomin tsaro su taimaka ma ta wajen kawar da ɓata garin ’yan jaridu a cikin su.

Sanarwar ya fito ne a ƙarshen taron da ƙungiyar ta yi a ranar 14 Oktoba 2021, inda ta ƙara da nuna buƙatar ta na samun cikakken jagoranci kamar yadda take gudanar da aikinta na ƙasa.

Ƙungiyar ’yan jaridu ta Nijeriya reshen Zariya ta yi kira ga masu kula da tsaro da su taimaka wajen tsaftace harkar aikin jarida da kuma cire masu kiran kansu ’yan jarida wanda ba su dace ba.

Ta ci gaba da nuna ɓacin ranta wajen samun hauhawar masu ma aikin jarida karan tsaye a kafafen sada zumunta da kuma ’yan jaridan da basu cancanta ba.

Ƙungiyar ta nuna matuƙar alhininta ta yadda musamman ’yan siyasa suke goyan bayan masu amfani da kafafen sada zumunta da wasu kafafen watsa labarai wajen watsa magan ganu marasa daɗi da kuma labaran ƙarya.

Ta ƙara da gargaɗin masu dillancin labarai da su kiyaye ba da tattaunawa ga wakilan kafafen watsa labaran da basu inganta ba, ko kuma ɗaukar hukuncin da aka yankewa yin hakan.

Bugu da ƙari, ta yi duba akan lamuran tsaro a jihar kaduna da ta ɗauka matakin dakatar da ayyukan ta addanci da ’yan fashin daji a ciki da wajen Jihar wajen hana adaidaita sahu da kuma dakatar da babur na haya a Jihar.

Ta ƙara yin kira da hukumomin tsaro da su ruɓanya ayyukansu wajen sauya matsalolin da yake addabar ’yan Jihar.
Har ila yau sanarwar ta nuna matuƙar farin cikin ta ga gwamnatin jihar kaduna da hukumomin tsaro wajen nuna rashin gajiyawa ta fuskar dakatar da ayyukan ta’addanci.

Ta kuma ƙara da riko akan hukuncin da gwamnati Kaduna ta ke yi na magance tsaro da ta sake duba akai domin sassautama masu mashina na kansu domin gudanar da ayyuakansu na musamman.

A ƙarshe qungiyar ta taya mai martaba sarkin Zazzau, Malam Ahmad Nuhu bamalli murnar cika shekara ɗaya, tare da jinjina masa akan gagarimin nasarorin da aka samu a cikin shekararsa ɗaya akan karagar mulki.

Sanarwar ta qara da bayyana fatan ta na samun wasu cigaban a shekarunsa na gaba akan karagar mulki.

Ƙungiyar ta rufe jawabin da naɗa kwamitin mutane uku 3 wanda tasama jagoranci daga Mika’il Ibrahim Fagaci na gidan redio nagarta da ke Kaduna, domin samun nasarorin ƙungiyar a zaɓen da za ta gudanar nan gaba na watan Nowambar wannan shekarar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *