Akwai dalilanmu na shirya wa ɗaliban firamare muhawara kan Korona – Ƙungiyar CAGSI

Daga MUHAMMADU MUJITABA

Shugabar ƙungiyar CAGSI ta ƙasa da ke da ofishi a Kano, Hajiya Maryam Garba Usman ta bayyana cewa, akwai dalilai masu yawa da yasa suka shirya muhawara kan cutar korona ga ɗaliban makarantun firamare takwas da suka zaɓo daga ƙananan hukumomi huɗu a cikin ƙwaryar birinin Kano wanda aka gabatar a ranar Litinin ta makon jiya a harabar ɗakin taro na hukumar Ilimi bai ɗaya a Kano.

A farko shugabar ƙungiyar ta CAGSI ta ce, ganin yadda wannan cuta ta ɓullo wa duniya a ƙarshen shekarar 2019 ta kuma mamaye duniya ya sa aka yi ta wayar da kan jama’a amma manya ba yara ba to shi ne yanzu CAGSI ta shirya mahawara akan yadda su ma yara za su santa da kuma yadda za su yaƙe, wanda hakan ne yasa aka shiryawa ‘yan firamare ‘yan shekara 14 zuwa ƙasa muhawara akan korona ƙarya ce? ko gaskiya? Da kuma gasar iya ɗinka takunkumin korona kuma suka fafata a tsakaninsu domin su yi tunani akanta duk da an san korona gaskiya ce illa dai dan su san abun da ya kamata na Korona.

Muhawarar, wanda ta kasance a tsakanin firamare biyu daga ko wace qaramar hukuma huɗu da ƙaramar hukumar Nasaraw wacce ta zamo ta ɗaya a muhawarar korona sai Kumbotso ta zama ta biyu a nasarar sauran ƙananan hukumomin da suka shiga su ne Fagge, Dala, haka kuma a gasar iya ɗinka takunkumi fuska a ɗaya ɓangaren na muhawarar da CAGSI shirya duka a ranar, Kumbtso ta zo ta farko a wajen ɗinka takunkumi rufe fuska da akayi duk a wannan lokaci.

Adamu Abubakar ne ɗalibin da ya samu nasara daga Nasarawa, Fatima Kabir da Hasiya haka ɗaliban Kumbotso da Nasarawa da sauran ƙananan hukumomin da suke shiga su samu rakiyar malaman su dan fafata muhawara da aka yi irin su Rabiu Mustapha daga dala da sauran su.