Akwai haƙƙin al’umma da ke kan kowanne ɗan jarida – Zainab Bala

“Ina ɗaya daga cikin mata uku da Cibiyar ’Yan jarida ta Duniya ta karrama”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Hajiya Zainab Bala ɗaya ce daga cikin matasan ‘yan jarida da tauraruwar su ke haskawa ba ma a Arewa kaɗai ba har ma da duniya bakiɗaya, kasancewar ta daga cikin fitattun mata ‘yan jarida uku da Cibiyar ‘Yan Jarida ta Duniya (ICJ) ta karrama da shaidar yabo ta ‘Michael Elliott’ ta shekarar 2021, saboda yadda aikin su ke taimaka wa wajen inganta rayuwar raunananu a cikin al’umma. Jajircewa da aiki tuƙuru sun taimaka wajen buɗe mata hanya ta kai ga matakai da dama a ‘yan shekaru ƙalilan da ta shafe tana aikin watsa labarai da shirye-shiryen talabijin. A zantawarta da Manhaja, ‘yar jaridar ta bayyana abin da ya ja hankalinta ta shiga aikin jarida har kuma ta zama mai taimaka wa mutane.

MANHAJA: Ko za ki gabatar mana da kanki?
ZAINAB: To, da farko dai sunana Zainab Bala, ‘yar jarida, matar aure kuma uwa. Mahaifina ɗan asalin Jihar Kano ne, mahaifiyata kuma ‘yar asalin Jihar Naija ce. Na taso, na yi karatuna tsakanin Abuja da Jos. Na fara karatun aikin jarida ne a Kwalejin Talabijin ta NTA da ke Jos wacce ke ƙarƙashin jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Na fara koyon sanin makamar aiki a tashar NTA ‘Channel’ 5 da sashin NTA ‘International’ a babbar hedkwatar talabijin ta ƙasa da ke Abuja. Na kuma yi aikin hidimar ƙasa a tashar talabijin ta GOTEL da ke Yola a Jihar Adamawa. Na taɓa aiki na wasu shekaru a tashar Viewer TV, kafin daga bisani sabuwar tashar Trust TV da ke ƙarƙashin kamfanin Media Trust masu buga jaridun ‘Daily Trust’ su neme ni, don in yi aiki da su, bayan nazarin cigaban da na samu a aikin jarida. 

Kafin mu zo ga nasarorin da kika samu, ko za ki gaya mana abin da ya fara jan hankalinki ga aikin jarida? 
To, alal haƙiƙa tun tasowa ta ina yarinya na kasance mai sha’awar kallon TV, musamman ina son kallon labaran mata ‘yan jarida, yadda suke kwalliya suna labarai da Turanci yana burge ni sosai. Na girma da tunanin wata rana nima zan iya zama mai karanta labarai. Ko da yake a zuciyata na fi son a ce na zama mai arziƙi ko mai wata dama da zan riƙa yin ayyukan jin ƙai na taimaka wa jama’a. Sai bayan da na girma ne a makaranta na fahimci ashe da aikin jarida ma zan iya zama mai amfani ga al’umma. 

Kin kasance mai gabatar da shirin ‘The Scoop’ wanda ke zaƙulo wasu matsaloli na rayuwa, ana nema mu su mafita da sauƙi. Mai ya ja hankalinki wajen ƙirkiro da wannan shiri? 
Babu shakka zan iya cewa shirin ‘The Scoop’ shi ne cikar burina na son taimaka wa mabuƙata, shi ne kuma ya zama sanadin samun ɗaukaka ta. A dalilin shirin ‘The Scoop’, na canza rayuwar mutane da dama. Saboda na fahimci aikin jarida ba ya tsaya ne kawai kan bayyana ayyukan gwamnati da magana cikin ƙayataccen Turanci ba, akwai hakkin al’umma da ke kan kowanne ɗan jarida na bayyana wa duniya irin ƙalubalen da suke fuskanta da tattauna yadda za a taimaka mu su. Ta cikin shirin da na ke gabatarwa, an samu wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu da wasu hukumomin gwamnati sun ba da gudunmawa sosai wajen share hawayen wasu da shirin ya tattauna a kansu.  Ba na mantawa da wata yarinya Aisha mai ɗauke da wata lalura ta nakasa, iyayenta ba masu hali ba ne, kuma tana son ta yi karatu, saboda rashin ƙarfin iyayen sai bara ta koma yi a titi. A dalilin shirin da na yi a kanta Gidauniyar Maggie Cares ta ɗauki nauyin karatun ta na firamare har ta gama. Akwai wani yaro kurma wanda aka riqa zargi da yi wa yara luwaɗi a makarantar yara kurame da ke nan Abuja, mutane na ta nuna masa ƙyama da hantara, amma bayan wani shiri da mu ka yi a kansa sai aka samu sauƙin abin da ake yi masa, ya kuma ci gaba da rayuwar sa kamar sauran yara. Ire-iren waɗannan na nan da kullum na tuna na kan gode wa Allah da ya sa ta dalilina wasu suka yi dariya. 

Wane ƙalubale za ki iya cewa mata ‘yan jarida suke fuskanta wajen gudanar da ayyukansu?
Eh, gaskiya mata ‘yan jarida na fama da ƙalubale iri iri a wuraren ayyukan su da cikin al’umma. A ‘yan shekarun da na yi ina aiki na lura ba a bai wa mata manyan matsayi a wajen aiki, sannan ba a tura su ɗaukar rahoto a wasu wuraren, kamar misalin abin da ya shafi siyasa ko wasannin ƙwallon ƙafa. Ana ganin ba fagen mata ba ne, ko da kuwa akwai matan da suke da sha’awar harkokin siyasa. A ganina bai kamata a ce ana ware mata, don ana mu su kallon suna da rauni. Ni na san akwai haziƙan mata ‘yan jarida da suke da burin kai wa kowanne mataki da shiga kowanne lungu, don gudanar da aikin su. 

A matsayin ki ta matar aure kuma uwa, yaya kike haɗa aiki da hidimar iyalinka?
Aiki da iyali, abubuwa ne masu muhimmanci a rayuwa, ba zai yiwu ka ɗauki ɗaya ka bar ɗaya ba. Abu muhimmi shi ne a ce mace ta samu miji mai fahimta da sauqin kai, wanda zai ba ta tallafi da goyon baya, don cimma burin ta na rayuwa. Don haka zan iya cewa na gode wa Allah da na samu iyali masu fahimta, duk nasarar da na samu a rayuwa a dalilin tallafin su ne. Duk lokacin da na ke da aiki a ofis na kan bar yarona a gida, aka kula min da shi. Wani ƙarin nauyin ma kuma yanzu ga karatun digiri na biyu da na fara, ga aikin ga kuma hidimar iyali. 

Wanne irin cigaba za ki iya cewa kin samu sakamakon aikin da ki ke yi?
Alhamdulillahi. Babu shakka na samu nasarori da yawa, babba daga ciki shi ne samun ɗaukaka a idon duniya ta dalilin wannan aiki, inda Cibiyar ‘yan Jarida ta Duniya (ICJ) ta ba ni shaidar karramawa, sakamakon tasirin da aikina ke yi a rayuwar wasu. Wannan ya taimaka min sosai wajen samun ɗaukaka a gida da waje. A saboda haka ne har tashar talabijin ta Trust TV ta ba ni aiki, kuma wata Gidauniyar Tallafa wa Mata ‘Yan Jarida ta bani tallafin wasu kuɗaɗe don gudanar da wasu ayyukan jin ƙai na taimakon al’ umma. 

Mene ne babban burinki nan gaba a wannan aikin da ki ke yi?
Ina da burin kafa gidauniyar tallafa wa mata da qananan yara, ƙarƙashin wannan shiri da na ke yi na ‘The Scoop’. Kuma ina son in samar da wata cibiya ta horar da yaran mata masu sha’awar aikin jarida. Ina da burin ganin na samar da canji a rayuwar wasu, ta dalilin aikin jarida. 

Mene ne saƙonki ga sauran matasa mata da ke da sha’awar wannan aiki da kuke yi?
Kafin ki shiga fagen aikin jarida ko karatu a fannin koyon aikin jarida, ki tabbatar da cewa, abin da kike son yi kenan. Domin akwai lokacin da idan abubuwa suka yi zafi, wannan burin da kike da shi ne kaɗai zai taimake ki. Sannan ina son in bai wa mata ƙarin ƙwarin gwiwa, kada su ɗauka cewa, akwai wani abu da su ba za su iya ba a dukkan aikin da suke yi. Don aikin jarida bai san maza ba ko mata. 

Zainab

Wanne abu ne ya fi vata miki rai a matsayin ki na ‘yar jarida?
Babu kamar cin rai da cin lokaci da aikin ke da shi. Aiki ne da yake cinye rayuwar mutum bakiɗaya. Sai kuma matsalar samun mutanen da za ka yi hira da su, musamman ƙwararru a fannoni daban daban, ko wasu wakilan gwamnati. Abu ne mawuyaci ainun ka samu dama su ba ka lokacinsu. 

Wacce kwalliya ce ta fi burge ki? 
Gaskiya na fi son ɗinkin atamfa ko dogayen riguna na abaya, su na yi min daɗin sakawa. Kuma suna da tsari mai ban sha’awa kala-kala. 

Shin mutane kan miki kyauta ko wani alheri don jin daɗin aikin ki, kuma wacce kyauta ce kika fi sha’awar karɓa?
Sosai kuwa. Ina samun kyaututtuka da dama daga wajen mutane masoya da ke nuna jin daɗin su da aikina. Gaskiya ina son turare, kyautar turare, saboda Ina son ƙamshi sosai. 

Malama Zainab, muna godiya. 
Ni ma na gode ƙwarai da gaske.