Akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin hukumar NAYES da sauran hukumomin tsaro a Nasarawa – G.M Labaran Maina

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Janaral Manaja na hukumar tsaro na gwamnatin jihar Nasarawa wato Nasarawa Egency For Youth Empowerment Scheme (NAYES) a turance, Abdullahi Labaran Maina ya yi kira na musamman ga jami’an hukumar ta NAYES a jihar baki ɗaya su tabbatar suna cigaba da kasancewa jami’an hukumar nagari a duk inda suke gudanar ayyukansu a faɗin jihar.

Janaral Manajan, Abdullahi Labaran Maina ya yi wannan kira ne a lokacin da yake zantawa da wakilin mu a ofishinsa dake hedikwatar hukumar ta NAYES a garin Lafiya babban birnin jihar ranar Talata na makon nan da ake ciki.

Ya ce ba shakka an san jami’an hukumar da aiki tuƙuru da kuma bin doka da oda saboda haka dole ne su yi duka mai yiwuwa wajen tabbatar ba su ɓata wannan kyakkyawar suna da aka san hukumar da shi ba.

Ya ce hukumar wanda gwamnatin jihar ta kafa na da manufar aiki ne tare da sauran hukumomin tsaro daban-daban dake jihar inda sukan gudanar da sintiri ne da kuma cafke masu aikata laifuffuka su kuma gabatar da su ga sauran hukumomin tsaro a jihar don yanke hukunci da sauran su.

A cewar G.M. Abdullahi Labaran Maina akwai waɗannan jami’an su da dama a duka ƙananan hukumomin jihar 13 dake aiki tuƙuru ba dare ba rana don tabbatar ana bin doka da oda tare da agaza wa ‘yan sanda da sauran su wajen yaƙi da munanan ayyuka da sauran su.

Ya kuma yi amfani da damar inda ya bayyana wasu daga cikin ɗimbin nasarori da hukumar ta NAYES a jihar qarqashin jagorancinsa ta cimma kawo yanzu cewa sun haɗa da rage ayyukan ta’asa musamman tsakanin matasa da haɗa dai da sauran hukumomin tsaro a jihar don sauke nauyi dake wuyan su da gudanar da tarurruka akai-akai tsakanin hukumar da sauran masu ruwa da tsaki da masu unguwanni da nufin kawo ƙarshen ayyukan munanan laifuffuka da sauran su.

Dangane da ƙalubale da NAYES ɗin ke fuskanta a jihar Abdullahi Labaran Maina ya bayyana cewa ƙalubalen bai wuce na rashin isassun ababen hawa don gudanar da ayyukan su ba.

Kodayake a cewarsa a ‘yan kwanakin nan hukumar ta rubuto wa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule dangane da buƙatar inda ya kuma amince tare da tabbatar musu cewa nan bada daɗewa ba idan za a fara rabon ababen hawan ga hukumomin tsaron jihar duka suma za a ba su nasu.

Daga nan sai Janar Manajan hukumar ta NAYES a jihar Abdullahi Labaran Maina ya yi amfani da damar inda ya buqaci haɗin kai na musamman tsakanin al’ummar jihar baki ɗaya da hukumar sa ta NAYES ɗin inda ya ƙara jajanta cewa da zarar wani ko wata ya ji ko ya ga wani abu da ka iya zamo ƙalubalen tsaro a jihar sai a yi maza a tuntuvi hukumar ta lambar wayarsa da aka riga aka sanar wa al’umma.

Binciken wakilin mu dai ya gano cewa a yanzu haka al’ummar jihar ta Nasarawa na cigaba da yaba wa Janar Manajan hukumar tsaron ta NAYES a jihar Abdullahi Labaran Maina dangane da sabbin dabarun yaƙi da masu aikata laifuffuka da yake aiwatar ta hukumar da hakan ya sa a yanzu haka al’ummar jihar na barci da idanuwansu a rufe ba tare da fargaba ko tsoro ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *