Akwai kyakyawar alaƙa tsakanin marubutan Nijar da Nijeriya – Saratu Alqasim

“Akwai masu sha’awar yin rubutun Hausa sosai a Ƙasar Saudiyya”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Harshen Hausa na daga cikin manyan harsunan duniya waɗanda suke cigaba da bunqasa da yaɗuwa, sakamakon safara da kasuwanci da Hausawa ke yawan yi a tsakanin ƙasashen duniya, da kuma rubuce rubucen littattafai da marubuta ke yi cikin harshen Hausa, da ke yawo a tsakanin mata da matasa da ke rayuwa a wasu ƙasashe. Daga cikin Hausawa da ke zaune a Ƙasar Saudiyya, akwai wata marubuciya ýar asalin Ƙasar Nijar da tauraruwarta ke haskawa a tsakanin marubutan adabi a Nijeriya, saboda baiwar da Allah ya yi mata na sarrafa labari cikin hikima a salon nishaɗi, almara da kuma soyayya, wanda hakan ya mayar da ita daban cikin marubuta. A zantawar da ta yi da wakilin Manhaja, a Jos, Saratu Alqasim da aka fi sani da Maman Nusaiba ta bayyana yadda ta fuskanci tsangwama a wajen wasu mata marubuta, kafin tauraruwarta ta fara haskawa.

MANHAJA: Za mu son jin taƙaitaccen tarihin marubuciyar?

MAMAN NUSAIBA: Assalam Alaikum. Ni dai asalin sunana Sarat Alqasum, wacce aka fi sani da Maman Nusaiba a duniyar marubuta. Ni yar asalin Jamhuriyar Nijar ce daga Jihar Magarya, sunan garinmu Maimadjè. An haife ni a shekarar 1998, yanzu Ina da shekara 24 a duniya. Na yi karatuna na boko da Islamiyya a cikin garinmu. Daga bisani na ci jarrabawa na shiga mataki na gaba wato sakandire C.E.J, Ina shekarata biyu ne kuma aka tayar da maganar aurena, dole na ajiye karatu aka tafi ibada.

Mai za ki iya tunawa game da yadda ki ka taso yayin ƙuruciya?

Gaskiya rayuwar quruciya akwai daɗi, don kuwa na sha ɗaukar magana ba kaɗan ba. Ina iya tunawa a lokacin da nake ƙarama na addabi mutane ni da ƙanena a garinmu, kullum ana kawo kashedi gidanmu, maimakon mu fasa in aka zanemu sai mu yi abin da ya fi na farko. Kuma kasancewar na girma ne a hannun kakata sai rashin jin ya yi yawa.

Ba na mantawa akwai watarana na zane wani yaro ɗan qanen babanmu saboda ya ja min gashi, shi ne sai mamansa ta kai kashedina wajen kakata Hajja, Ina dawowa ta zaunar da ni ta ce, ‘da kin fita ki lallasa min shi tun da har ita uwar tashi ba ta da kunya ta kawo mini kashedi.” Ni kuwa Ina fita na sake zane shi, mamansa ta sake kawo ƙara, a gabanta na kama shi na sake duka. Hajja na cewa na masa dukan mutuwa, a dole mamansa ta haƙura. Duk lokacin da na tuna da wannan abin Ina yin dariya ko da yaushe. Allah sarki Hajja ta Allah ya miki rahama.

Me ya ja hankalinki har ki ka fara sha’awar rubuce rubuce?

To, a gaskiya dama ni na kasance ma’abociyar son karance-karancen littattafan Hausa ce daga na yaƙi har na soyayya da na aljannu duk Ina karantawa tun Ina ƴar shekara 13. Hakan ya ja hankalina har na ji zan iya yin rubutu. Kuma kamar da wasa na rubuta littafina na farko mai suna ‘Hafsat’ a manhajar Facebook a cikin wani zaure mai suna Ciwon ‘Ya Mace a shekarar 2019.

To, kawo yanzu kin rubuta littattafai sun kai nawa? Ba mu labarin wasu a taƙaice.

Na rubuta littafi guda tara, su ne: ‘Amir da Amira’, ‘Aljanar Jarumai’, ‘Hafsat’, ‘Ƙaddara Ce’, ‘Tani Da Manu’, ‘Rayuwar Ma’aurata’, ‘Sumayya Baiwar Allah’, sai ‘Abba Ne’ da ‘Aljanar Gidanmu’.

Shi littafin Aljanar Jarumai labari ne akan wata aljana Musulma wadda take taimakon bil’adama da ma aljanu. Ta haka ta haɗu da Husna wadda matar uba take gana mata azaba kamar ba gobe, darasin cikinsa yana nuna illar shiga bokaye da yadda ƙarshen mutum yake kasancewa. Sannan yana nuni da taimako abu ne mai kyau a ko’ina.

Shi kuma littafin ‘Abba Ne’ labari ne kan rayuwar wani jajirtaccen soja ɗan kishin ƙasa. Littafin yana nuni ne kan duk abin da za ka yi a ko’ina to, ka kasance ka na yi da gaskiya da kuma kishin ƙasarka da mutanen cikinta. Sannan yana nuni da yadda masu siyasa ke koyawa ƙananan yara shaye-shaye da illar da yake haifarwa, a ƙarshe kuma yana nuna zalunci da cin dukiyar da ba na kai ka halaka.

Littafin ‘Ƙaddara Ce’ kuwa labarin wasu ýan mata uku ne da ƙaddarar rayuwa ta kai su ƙasar Saudiyya. Labarin yana nuni ne a kan yadda rayuwa a Saudiyya take da yadda mutanen da ke wajen ƙasar ke kallon duk macen da ke Saudiyya a matsayin karuwa. Ƙaddara ta kawo su kuma sun fuskanci ƙalubalen rayuwa yadda ake kallonsu da irin wahalhalun da suka sha.

Shin akwai Hausawa masu sha’awar rubutun adabi a ƙasashen Larabawa ko nan Saudiyya?

Ba za a rasa ba, kodayake ba lallai ne in san su sosai ba. Amma a nan Saudiyya inda nake da zama, akwai masu sha’awar rubuce rubuce sosai, sai dai rashin samun wanda zai ƙarfafa su ko koyar da su sanin ka’idojin rubutu yadda su ma za su shiga cikin marubuta, kamar ni yadda nake alfahari da kasancewa ta marubuciya, duk da ba a Ƙasar Hausa nake zaune ba. Ina dai yin iya nawa qoqarin na fahimtar da waɗanda suka nunar min da sha’awar su a fili, wajen ba su shawarwarin da suka kamata.

Wanne ƙalubale ki ka fuskanta yayin fara shigowar ki duniyar marubuta?

To, ai ita rayuwa dama dole sai da ƙalubale a cikinta. Na fuskanci ƙalubale a harkar rubutu farkon fara rubutuna, saboda a lokacin ban tava ganin wani marubuci ko marubuciya ba, ko da kuwa a cikin ƙawaye ne. Babban ƙalubalen da na fuskanta fara rubutuna daga wajen ‘yan’uwana ne, da na ce musu nima fa Ina rubuta labari irin wanda muke karantawa sai su ce taya ma zan iya yin irin wannan labarin masu rubuta littafi sai sun yi digiri sun gama sanin komai a kan boko kana suke yi, maganar su ce ta sagar min da gwiwa matuƙa a lokacin Ina rubutu a takarda, na rubuta wani littafi da na ba shi suna ‘Yanayin Rayuwa’ hakan ya sa na ji na daina sha’awar rubutun na kasa cigaba rubutawa.

A 2019 ne na haɗu da wani sai muna hira nake ce masa da littafi nake son rubutawa sai ya ce ai kuwa abu ne mai kyau, a taƙaice dai shi ya bani ƙwarin gwiwa na ci gaba da rubutuna kuma har ila yau shi ne yana ci gaba da bani ƙwarin gwiwa a kan rubuce rubucen da nake yi. Ƙalubale na biyu, bayan na shigo harkar rubutu na tava samun matsala da wata marubuciya ban san me na yi mata ba, haka kawai duk inda ta ganni sai ta riƙa jefa min baƙaƙen maganganu, ni kuma bana son tashin hankali a lokacin abin sai yake damuna. Amma yanzu kam alhamdulillahi, ni ma na zama ýar gari a cikin marubuta, Ina cikin zaurukan marubuta da dama kuma muna zumunci da su, ana girmama juna.

To, a yanzu da ki ka saba da marubuta menene yake ba ki sha’awa game da mu’amalarki da su?

Abin da yake bani sha’awa game da marubuta a mu’amala ta da su gaskiya shi ne yadda muke ganin mutuncin juna, abin yana burge ni, wasu sukan ba ka shawara a kan rubutu, wasu kuma a wasa ƙwaƙwalwa akan harkar rubutu ana ƙaruwa da juna.

Yaya ki ke kallon dangantakar marubutan Najeriya da na Nijar, wajen zumunci da haɗin kai?

Kai gaskiya akwai kyakyawar alaƙa sosai a tsakanin mu da marubutan Najeriya sosai da sosai, muna zumunci da girmama juna a tsakanin mu. Babu raini ko cin mutuncin juna. Alhamdulillah.

Su waye fitattun ƙawayenki a cikin marubutan Nijeriya?

Babbar ƙawata dai ita ce Kyauta Daga Allah wato Iƙilima Adam, sai kuma Maman Amatullah, da Hafsat (Autar Mama).

Cikin rubuce rubucen da ki ka yi kin tava buga wani daga cikin littattafanki ne?

Gaskiya ban taɓa fitarwa ba. Saboda ba a Najeriya ko gida Nijar nake zaune yanzu, amma saboda cigaba da aka samu yanzu a harkar ɗab’i, in sha Allahu a wannan karon na samu dama nan da wani lokaci kaɗan littafina mai suna ‘Abba Ne’ zai fito kasuwa.

A cikin littattafanki, wanne ne za ki ce ya zama bakandamiyarki, wato wanda ki ka fi ji da shi?

Ai duk littattafaina ina ji da su sosai. Amma bakandamiyata littattafai biyu ne, waɗanda na fi ji da su. ‘Tani Da Manu’ sai ‘Abba Ne’.

Wanne canji ki ke ganin an samu a duniyar adabi sanadiyyar fitowar marubutan yanar gizo na online?

Rubutu a online cigaba ya kawo sosai da sosai, domin a da sai ka je kasuwa za ka iya sayen littafi, amma a yanzu kana zaune za ka sayi littafi ka karanta, an samu cigaba ba kaɗan ba. Sannan a dalilin rubutun da ake yi a online an samu bayyanar sabbin marubuta irin mu, waɗanda a da ba mu tava tunanin za mu iya rubuta littafi ba, ko ma a kira mu da marubuta ba. Sabbin tunani da sabbin jini sun bayyana, duk da yake dai har yanzu ba a kai ga samun cigaban da ake buƙata ba, saboda rashin ƙwarewa da sanin ƙa’idojin rubutu, kuma akasarin mu matasa ne, da ba mu samu gogewa sosai a kan rayuwa ba.

A tun farkon fara rubutunki wacce marubuciya ko marubuci ne ya fara ɗora ki a hanya yadda za ki fara gogewa, kuma rubutun wanne marubuci ne yake ɗaukar hankalinki?

Wacce ta tava koya min rubutu a online ita ce marubuciya Hafsat (Autar Mama) don ita ta fara nuna min yadda zan yi rubutu mai kyau, har na fara fahimtar ƙa’idojin rubutu daidai gwargwado. Kuma a gaskiya salon rubutun mutane da dama yana matuƙar birge ni kamar rubutun Hajara Ahmad (Oum-Nass) Jibrin Adamu Rano, Hadiza D. Auta, Ayuba Muhammed Ɗanzaki, Ikilima Adam, da kuma Hassana Labaran Ɗanlarabawa. Salon waɗannan mutanen yana matuƙar ɗaukar hankalina sosai.

Akwai wani abu na jin daɗi ko farin ciki da ya taɓa faruwa da ke a matsayinki ta marubuciya da ba za ki tava mantawa da shi ba?

Na tava yin wata nasara wacce ba zan taɓa mantawa da ita ba. A littafina mai suna ‘Hafsat’ wata ƴar nan Saudiyya ta karanta sai ta ɗauki lambata ta kira ni ta ce min ni ce na rubuta littafin Hafsat na ce, e. Sai ta ce tana so na mata kwatance ta zo gidanmu a lokacin ba na Makkah na tafi ziyara Madina, muka yi da ita bayan kwana biyu za ta zo gidanmu. Ta zo da ƴan gidansu kowa yake ta mamaki wai ni na rubuta littafin na ce musu sosai ba, ban zata ba na ga suna ta fiddo da kuɗi da turaruka na jiki da mayukan gyaran fata suka ajiye min. Na yi farinciki matuƙa a ranar.

Banhon littafin ‘Ƙaddara Ce’

Wacce ƙungiyar marubuta ki ke, kuma wanne alfanun ki ke samu daga kasancewarki mamba a cikin ta?

E, gaskiya Ina da ƙungiya mai suna Jarumai Writers Association, kuma Ina alfahari da ƙungiyar nan, domin sanadiyyar ta ne na sake samun gogewa da sanin ƙa’idojin rubutu, hulɗa da sauran marubuta maza da mata, da sanin muhimmancin kaina a matsayin marubuciya da yadda zan bayar da gudunmawata don cigaban al’umma baki ɗaya.

Wace shawara ki ke da ita ga matasan marubuta masu tasowa?

Yana da kyau marubuta su mayar da hankalinsu a kan halin rayuwar da muke ciki a wannan lokacin. Su riƙa yin rubutun da zai tava zuciyar kowa tare da kawo shawarwari ko mafita ga ƙalubalen rayuwar da ake ciki. Sannan idan za su yi rubutu su tsaftace alƙalaminsu su riƙa yin rubutu mai inganci wanda babu batsa a cikin sa su kuma kiyaye da bin ƙa’idojin rubutu Hausa.

Wace karin magana ce take tasiri a rayuwarki?

Kowanne tsuntsu kukan gidan su yake yi.

Mun gode.

Ni ce da godiya. Allah ya saka da alheri.