Akwai masifu da dama fiye da rashin yin zaɓe – Martani ga Ɗansadau

DAGA ABDULWAHAB SULAIMAN

A wata sabuwar tattaunawar Sanata Ɗansadau ya sake yi da BBC Hausa game da korar Digital Iman din da suka yi daga Limancin Masallacin rukunin gidajen ‘yan Majalisa dake Apo Legislative Quaters, Abuja.

A hirar tasu ya bayyana cewa, wai mutane ba su san masifar rashin yin zaɓe ba. Akwai masifar da ta kai, ‘yan  bindiga su shiga gari su kashe mutane, su sace musu dabbobi, su sace Yara, kuma su yi wa mata fyaɗe. Akwai wani bidiyo da na gani na wata tsohuwa ‘yar kusan shekara 70 tana kuka tana cewa wani yaro ɗan bindiga ya yi mata fyaɗe. 

Akwai masifar da ta kai, kana kwance a gida wasu mutane su zo, su kama harbinku, su kashe ku, su yi garkuwa da wasu, sannan su tafi. Akwai masifar da ta kai a yi wa yarinya fyaɗe a gaban iyayenta? Akwai masifar da ta kai a yi wa uwa fyaɗe a gaban mijinta da ‘ya’yanta?

Akwai masifar da ta kai mahaifi ya kai ‘yarsa makaranta, amma ‘yan bindiga su je, su kwashe su, su tafi daji da su, su aurar dasu a tsakanin su? Akwai masifar da ta kai mutane suna tafiya a Mota a tare su a kunnawa motar tasu wuta suna ciki gabaɗaya su ƙone a cikin motar? Akwai masifar da ta kai mutane suna gona a je a yi musu yankan rago?

Akwai masifar da ta kai mutum yana gidansa tare da iyalinsa, amma lokaci ɗaya, a zo a kore su daga garinsu, a ƙona musu gonaki, sannan a mayar da su ‘an gudun hijira? Akwai masifar da ta kai mutum yana tafiya a hanya, a tare shi a tafi cikin daji da shi, sannan a kira ‘yan uwansa a ce sai sun biya miliyoyin kuɗi, sannan za a sake shi?

Duk waɗannan ba masifu ba ne a wajen Sanata Dansadau, babbar masifa a wajensa ita ce, mutane su zauna a gida su ce ba za su yi zabe ba. Saboda idan hakan ta faru,  wataƙila zai iya rasa kujerarsa ta mulki.

Muna roƙon ALLAH ya kawo mana ƙarshen wannan matsalar ta rashin tsaro da ta addabi yankinmu na Arewa.

Sulaiman ɗan Nijeriya ne mai bayyana ra’ayi.