Akwai matsalolin da ke ci wa marubuta tuwo a ƙwarya birjik – Faisal Hunƙuyi 

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

MANHAJA: Yaya alaƙarka take da sauran marubuta?

FAISAL HUNƙUYI: Akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanina da marubuta, domin su ɗin dangina ne. Muna zumunci, mu yi wasa da dariya. Sannan akwai mutunta juna a tsakaninmu.

Sannu a hankali harkar talifin littattafai na takarda yana dawowa, yaya kake jin za a farfaɗo da kasuwancin littattafan Hausa?

Dawo da kasuwancin littafi kamar na shekarun da suka gabata ba abu ne da zai faru cikin sauƙi ba. Ta wani ƙaulin ma zan iya cewa ba zai yiwu a koma kamar yadda ake a baya ba, domin ba a ɓari a kwashe gabaɗaya. An samu cigaba, amma ta wani fannin zan iya kiranshi da ci gaban mai haƙan rijiya. Yayin da ta wata fuskar kuma zan kalle shi a matsayin cigaba mai amfani. Da a ce gabaɗayanmu marubuta tun daga na onlayin har masu bugawa a takarda za mu ɗinke mu yi magana da murya ɗaya tak! Sautinmu ya karaɗe kunnuwan makaranta rubutunmu mu nuna masu cewa; rubutu fa daraja gareshi ba a samun shi da sauƙi ma’ana dai mu daina bayar da shi a kyauta, kamar yadda cigaban zamani ya karanta mana. Ko da za mu yi dillancin labaranmu a onlayin ya kasance suna biyan wani abin hasafi, kafin a samu damar kai wa ga rubutun.

Sannan, mu inganta rubutunmu ta yadda za mu iya neman jami’o’i da kwalejoji su sanya littafin mu a jadawalin karatun ɗalibai, hakan zai ƙara taimakawa wajen habaka kasuwancin littattafan da aka buga a takarda.

Wanne tsarin rubutun ne ya fi burge ka, tsakanin onlayin da na littafi?

Ina ɗora labaraina a onlayin, amma ni a karan kaina gaskiya tsarin littafi ya fi burgeni, domin bana iya jure karatu a onlayin.

Kana ganin maza marubuta adabi na samun tasiri kuwa, duba da yadda mata marubuta suka ƙwace harkar?

Suna samu kam sai dai mafi akasarin tasirin na su ya ta’allaka ne da abin da suka rubuta. A baya lokacin kasuwancin littattafai na garawa sosai, akwai marubuta maza da yawa da ke ba da gudunmawa, yanzu kuwa da aka zo zamanin da harkar littafin ba ta kaiwa yadda ake so da yawan na da ɗin ma sun fara sakin harkar suna kama wasu harkokin. Akwai maza masu basira da hikimar rubutu sai dai yanayin aiki ko uzurorin rayuwa ya dankwafar da wannan hikimar tasu duk da cewa abin na cikin ransu.

Shin kana da sha’awar rubutun fim? Ko ka taɓa rubutawa?

Ina da sha’awa sosai, sai dai har yanzu ban kai ga rubutawa ba. Amma ina hanyar farawa, in sha Allah. 

Idan ka samu dama wanne abu za ka iya sauyawa a harkar rubutun adabi da talifi?

Akwai matsalolin da ke ci wa marubuta tuwo a ƙwarya birjik, amma matsalar da nake hangenta a babbar matsala duk da wasu za su kalle ta a ba ta kai ta kawo ba, bata wuce matsalar ‘yan downloading’ ba. Idan na ce ‘yan downloading’ ina nufin masu zuwa su ɗauki littafi ba tare da izinin marubuci ko marubuciyar ba, su karanta shi da muryoyinsu, domin gyara tukunyar gidansu. Ka ga a nan an yi kura da shan bugu gardi da kwasar kuɗi kenan. 

Idan ka je YouTube za ka samu littattafan marubuta sosai waɗanda ba su da masaniyar yadda aka fara karantasu har aka ɗora a YouTube ɗin ma. Wannan ba ƙaramin koma baya ba ne ga marubuta duk da salo ne na ci gaban zamani. Kuma samun ‘audio’ ɗin da ake yi ya taka muhimmiyar rawa wajen daƙile karatu a takarda ko a onlayin din ma.

A mahangata hukumomin da abin ya shafa ya kamata su yi tsayin daka wajen daƙile yawaitar wannan matsalar kamar yadda ‘yan fim suka dinga fafutuka a lokacin da suka fuskanci makamanciyar wannan matsala ta satar fasaha.

Na biyu; Yadda kasuwar littafi ke tafiya a onlayin ɗin shi ma akwai gyara sosai domin ni har na gwammace ma in samu masu siyen labarina a takarda in buga in ba su su bani sulallana akan in kai shi onlayin. Dalilina kuwa shi ne; marubuci ko marubuciya za su bata dare wajen tsara rubutunsu a karshe a onlayin ɗin idan ba za su bada na bulus ba bai wuce mutum uku zuwa biyar ne za su iya cire kuɗi su siya, waɗannan mutane biyar ɗin idan su ka siya to ki kaddara tamkar kin sakarwa duniya labarin ne.

A wannan gaɓar in da zan samu dama zan kirkiri wata manhaja ce da za a riƙa saka littafi a ciki tana ba da lambobin sirri mabambanta (password) ta yadda idan Bala ya siya to lambobin da zai sa ya buɗe littafin ya bambanta da na Shehu. Sannan a cikin manhajar zan saka abin da zai hana littafin buɗewa a ko wacce waya face ainihin wayar da aka fara buɗe shi da ita. Faruwar hakan zai daƙile yawaitar tura labarin da aka siya ba tare da izinin marubuciyar ko marubucin ba.

Bayan karatu da rubutu wanne abu ne ya fi ɗaukar hankalinka?

Noma da kiwo sai kuma koyarwa. 

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarka?

ɗan hakin da ka raina shi ke tsole ma ido.

Na gode.

Alhamdulillahi. Ina godiya ƙwarai da gaske.