Daga BELLO A. BABAJI
Kakakin rundunar ƴan sandan Nijeriya, Muyiwa Adejobi ya ce kimanin Naira biliyan 9 aka tara don haddasa tashin-tashina a yayin zanga-zangar tsadar rayuwa da ta gabata a watan Agusta.
Adejobi ya bayyana hakan ne a yayin taron ‘Civil Space Guard’ da aka gudanar a Cibiyar aikin jaridar zurfafa bincike ta Wole Soyinka (WSCIJ) da haɗin-gwiwar Masarautar ƙasar Netherlands.
An gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwar ne daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta, 2024, wanda al’ummomin jihohin Nijeriya da dama suka tsunduma aciki.
An gudanar da zanga-zangar a kudancin Nijeriya cikin lumana yayin da lamarin a Arewaci kuma ya ƙazanta inda aka yi ta samun tarzoma a wasu jihohi.
Sannan, an ga wasu masu zanga-zangar su na ɗaga tutar ƙasar Rasha tare da kira ga Shugaban Vladimir Putin ya kawo ɗauki wa shugabancin Nijeriya.
Adejobi ya ce, kafin zanga-zangar, sai da ƴan sanda suka sanar da cewa akwai yiwuwar a sauya zanga-zangar zuwa tarzoma daga waje wanda al’umma da dama ba su yarda ba, ya na mai ikirarin su kan bayyana ababe da dama bisa bincike da su ke yi wanda akan ƙaryata su.
Ya ƙara da cewa yayin da wasu ke ƙoƙarin yin zanga-zanga don nuna damuwa ga halin matsin da suke ciki, wasu ko su kan yi amfani da damar hakan ne wajen samun kuɗi, inda ya ce lallai sun samu kuɗi kusan Naira biliyan 9 don haddasa fitina a Nijeriya.