Akwai ’yan adawar Tinubu a fadar shugaban ƙasa, inji El-Rufa’i

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya yi zargin cewa akwai masu ƙin ɗan takarar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar APC, Bola Tinubu a Fadar Aso Rock da su ke ƙoƙarin ganin sun kai shi ƙasa a zaɓe.

Ya bayyana haka ne yayin tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels, a cikin shirinsu na Sunrise Daily da safiyar Laraba.

El-Rufa’i ya ce, mutanen, waɗanda bai bayyana sunansu ba, sun fusata ne tun lokacin da aka kayar da ɗan takararsu a zaɓen fidda-gwani na APC.

Ya kuma ce mutanen na fakewa da buƙatar ganin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi abin da ya dace.

Ya ce, “Na tabbatar a cikin Fadar Shugaban Ƙasa akwai masu son mu faɗi zaɓen nan, saboda buƙatarsu ba ta biya ba, an kayar da ɗan takararsu a zaɓen fidda-gwani.

“Waɗannan mutanen na ƙoƙarin fakewa da buƙatar Buhari ya yi abin da ya dace. Zan bayar da misalai biyu, wannan batun na biyan tallafin mai wanda ya ke sa Nijeriya ta kashe maƙudan kuɗaɗe abu ne da dukkanmu mun daɗe da amincewa a cire shi.

“Misali na biyu kuma shi ne canjin kuɗi. Ya kamata a fahimci Shugaban Ƙasa. Mutane na zargin Gwamnan CBN, amma ba haka batun yake ba. Idan muka koma tarihi, ko zamanin mulkin Buhari na soja, ya canka kuɗi saboda maganin ɓarayi da masu ajiye haramtattun kuɗaɗe a gida.

“Manufa ce mai kyau, kuma Shugaban Ƙasa yana da dalilansa na yin hakan, amma yin hakan cikin kankanin lokaci kuma ana tunkarar zaɓe bai da wani amfani,” inji Gwamnan.

Sai dai kuma, an jiyo Ministan Yaɗa Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed na cewa Gwamnati ba ta da masaniyar Tinubu na da ‘yan adawa. Fadar Shugaban Ƙasa.