Akwai yiwuwar ƙulla gagarimar maja a zaɓen 2027 a Nijeriya – NNPP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Jam’iyyar NNPP na ƙasa, Ajuri Ahmed, ya nuna akwai yiwuwar ƙulla gagagrimar maja da wasu jam’iyyun siyasar Nijeriya domin tunkarar zaɓen 2027 domin kawo ƙarshen mulkin Shugaba Tinubu.

Ahmad ya bayyana hakan ne a Akuren jihar Ondo a ranar Alhamis a yayin yaƙin neman zaɓen gwamnan jihar da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba mai zuwa.

Ya ce akwai tattaunawa game da yadda za a kawo ƙarshen mulkin jam’iyyar APC a zaɓen 2027.

Sai dai bai bayyana sunayen jam’iyyun da ake kan tattauna da su, inda ya ce idan aka kuma gaza cimma matsaya, to NNPP kai tsaye za ta tunkari zaɓen 2027 ba tare da ko gezau ba.

Ya kuma ce akwai yuwuwar jam’iyyar APC ta yi munamuna a zaɓen gwamnan da za a yi, inda ya ce amma yana da tabbacin al’umma za su kaɗa ƙuri’arsu, su kasa, su tsare.

A yayin gangamin, shugaban jam’iyyar NNPP na ƙasa ya miƙa wa ɗan takardar gwamnan jiha a jam’iyyar tasu tuta, Olugbenga Edema, tare da jan hankalin al’umma kan kar su lamunci wata katsalandan daga ‘yan jam’iyya domin kauce wa rikici.

Kuma ya ce ta hanyar haɗin kai da gaskiyar da aka san mutanen jam’iyyar NNPP ne, sa su iya kai wa ga gaci a zaɓen.

Shi ma ɗan takardar jam’iyyar NNPP, Edema, ya ce idan ya yi nasara, gwmanatinsa za ta tabbatar da ilimi kyauta a dukkan matakai na karantu kuma dole ga kowa a faɗin jihar.

Ya ce, akwai manufofi bakwai da gwamnatinsa za ta sa a gaba, wanda kuma ya yi wa take da, Munufofin jihar Ondo daga Allah, waɗanda za su ciyar da alumma gaba idan an kai ga zaɓarsa.

Sannan ya ce ƙarin tagomashin shi ne, zai ɓullo da tsarin kiwon lafiya kyauta da kuma tsare-tsaren da za su tabbatar da ‘yancin ƙananan hukumomi da raya karkara da bunƙasa tattalin arziƙin jihar.

Jam’iyyar APC ta mayar wa da shugaban jam’iyyar NNPP martani kan cewa akwai rigingimu a jam’iyyun adawa.

A cikin wani jawabi da darakatan yaɗa labaran APC, Steɓe Otaloro, ya fitar, ta ce sam ba ta hannu a rikicin jam’iyyun siyasa saɓanin iƙirarin da shugaban jam’iyyar ANPP ya yi a jihar.

Ya ce gwmanatin Shugaba Tinubu ba ta lokacin yin siyasa domin ta mai da hankali ne wajen sake fasalin tattalin arziƙin ƙasa kuma sam babu wani batun shirin tunkarar zaɓen 2027 da Shugaba Tinubu ke yi domin yanzu ya fara gwamantinsa.

Sannan ya tabbatar da cewa jam’iyyun adawa ne ke kunna wa kansu wutar rikici saboda rashin haɗin kai kuma batun lashe zaɓen gwamnan jihar Ondo mafarki ne NNPP ke yi domin shi ɗan takarar ɗan jam’iyyar APC kafin ya faɗi a zaɓen fiddo gwani na jam’iyyar.